…Maniyyata 4,151 ne zasu sauke farali bana daga Jihar Kebbi – Shema

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kebbi ta ce kimanin mahajjata 4,151 ne za su gudanar da aikin Hajjin bana daga jihar, kuma ta yi musu kyakkyawar shiri don yin aikin yadda ya kamata.Shugaban Hukumar Alhaji Abdullahi Imam Shema ne ya bayyana haka ga Aminiya a Birnin Kebbi inda ya ce hukumar za ta yi […]

…Maniyyata 4,151 ne zasu sauke farali bana daga Jihar Kebbi – Shema
…Maniyyata 4,151 ne zasu sauke farali bana daga Jihar Kebbi – Shema

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kebbi ta ce kimanin mahajjata 4,151 ne za su gudanar da aikin Hajjin bana daga jihar, kuma ta yi musu kyakkyawar shiri don yin aikin yadda ya kamata.
Shugaban Hukumar Alhaji Abdullahi Imam Shema ne ya bayyana haka ga Aminiya a Birnin Kebbi inda ya ce hukumar za ta yi wa mahajjatan kyakkyawar tanadin da aikin Hajjin bana zai zama abin alfahari ga mahajjatan jihar.
Ya bukaci goyon bayan maniyyatan domin tabbatar da gudanar da aikin cikin nasara, kuma ya yi kira ga maniyyatan su bi doka da oda sannan su zama masu da’a a kowane lokaci har su kammala aikin Hajjin.