Maniyyata 5,120 za su sauke farali bana a Jihar Kebbi
Hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Kebbi ta bayyana cewa kimanin mahajjata 5120 zasu samu gudanar da aikin hajjin bana daga jihar wanda kuma ta masu kyakkyawan shiri na ganin sun gudanar da aikin hajji yadda ya kamata tun daga nan Nijeria zuwa kasa mai tsalki.Bayanin hakan ya fit one daga bakin sabon shugaban hukumar, […]
Hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Kebbi ta bayyana cewa kimanin mahajjata 5120 zasu samu gudanar da aikin hajjin bana daga jihar wanda kuma ta masu kyakkyawan shiri na ganin sun gudanar da aikin hajji yadda ya kamata tun daga nan Nijeria zuwa kasa mai tsalki.
Bayanin hakan ya fit one daga bakin sabon shugaban hukumar, Alh. Abdullahi Imam Shema alokacin da yake zantawa da Aminiya a ofishinsa dake hukumar Alhazzai.
Alh. Abdullahi Imam ya bayyana cewar hukumar sa zata yiwa mahajjatan jihar kyakkyawar tanadi wanda zai basu damar gudanar da aikin hajjin su natsuwa da yanayi mai kyau.
Shugaban yaci gaba da cewa hajjin bana daga jihar Kebbi zai zama abun alfahari ga daukacin mahajjatan jihar baki daya yana mai bukatar goyon bayan su hadin kai domin tabbatar da cewa an gudanar da aikin cikin nasara.
A wani labari kuma, kimanin mabarata 800 ne suka daina sana’ar bara a jihar ta Kebbi, cikin shirin gwamnati na hana yawace-yawacen barace-barace a duk fadin jihar.
Mai baiwa gwamna shawara kan harkokin addini, Alhaji Abdullahi I. Shema shi ne ya bayyana haka ga manema labarai a ofishinsa da ke Birnin Kebbi.
Alhaji Shema ya ce hanyoyin da suke bi domin rage barace-barace a jihar, a karkashin wannan shirin, “Mukan dauko mutum uku a kalla daga kowace karamar hukuma daga cikin kananan hukumomi 21 na jihar, a kowace shekara, wanda idan ka hada zai ba ka 63, kuma idan ka kiyasta shekarun wannan hukumar daga 2000 zuwa yau, kimanin shekara 13 ke nan, wanda ya ba mu jimlar mutum 819 wadanda muka tabbatar sun daina bara sanadiyyar koya musu sana’o’i tare da kuma ba su jari.
A karshe Alhaji Shema yayi kira ga sauran hukumomi dake da alhakin talakawa, al’umma da kuma hana barace barace kamar su KESEPA watau hukumar kula da rayuwar al’umma ta jihar Kejji da ma’aikatar mata da sauran su da su raka kokari duk da yake dai baza a iya shiryar da kowa ba, duk yadda kayi kuwa, kuma wasu ko jarin nawa ka bau ba zasu daina bara ba sai sunje sunyi ya kuma shawarci wadanda basu bada sunayensu ba suyi kokarin zuwa karamar kuhumarsu su ba da sunayensu don tantancewa domin su sami shiga cikin shirin.