Maniyyata aikin Hajji 2 daga Kano sun rasu a hatsarin mota
Marigayi Alƙasim ya bar mata biyu da ’ya’ya bakwai, yayin da mahaifiyarsa ta bar ’ya’ya biyar.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta tabbatar da rasuwar wasu maniyyata aikin Hajjin bana su biyu a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a kan hanyar Rimin Gado zuwa Kano.
Waɗanda suka rasu su ne Alkasim Ibrahim Walawa mai shekara 48 da mahaifiyarsa Hadiza Garba mai shekara 73.
Rahotanni sun ce suna kan hanyarsu ta shirye-shiryen tafiya aikin Hajji a Saudiyya lokacin da hatsarin ya rutsa da su.
A sanarwar da Jami’in Hulda da Jama’a na hukumar, Sulaiman A. Dederi, ya fitar, ya bayyana cewa marigayin da mahaifiyarsa ’yan asalin ƙauyen Walawa ne a Karamar Hukumar Kabo ta Jihar Kano.
- El-Rufai: Kotu ta ɗage sauraron buƙatar beli zuwa watan Yuni
- Juyin mulki: Gwamnati ta maka waɗanda ake zargi a kotu
Alƙasim ya bar mata biyu da ’ya’ya bakwai, yayin da mahaifiyarsa ta bar ’ya’ya biyar.
Hukumar ta bayyana lamarin a matsayin abin baƙin ciki, inda ta ce sun rasu ne a lokacin da suke shirin tafiya ibada mai tsarki.
Hukumar ta yi addu’ar Allah Ya gafarta musu, Ya kuma sanya su cikin Aljannatul Firdaus, tare da jajanta wa iyalan da abin ya shafa, tana mai kira gare su da su yi haƙuri da juriya a wannan lokaci mai wahala.