Maniyyata masu dakko goro na kawo mana matsala —NAHCON

Maniyyata aikin Hajji daga Najeriya da ke tafiya da goro na janyo tsaiko wurin tantance su idan sun isa kasa mai tsarki

Maniyyata masu dakko goro na kawo mana matsala —NAHCON

Maniyyatan Kano

Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta koka kan yadda alhazan kasar ke ci gaba da safarar goro zuwa kasar Saudiyya.

Shugaban tawagar masu karbar baki na NAHCON a Madina, Labaran Abdullahi, ya ce shigo da goro na janyo musu kalubale, domin yana kawo tsaiko a tashoshin jiragen sama.

Labaran Abdullahi ya bayyana haka ne ga wasu zababbun ’yan jarida a Madina a ranar Lahadi.

Ya bayyana cewa hukumar ta bullo da sabbin tsare-tsare don tabbatar da kai maniyyata masaukansu cikin gaggawa daga filayen jiragen sama.

Ya kara da cewa wata matsalar ita ce yadda wasu maniyyata ke ajiye fasfo dinsu a cikin jakunkuna bayan an yi musu izini a Najeriya.

“Wasu daga maniyyatan sun  yi kuskure sun sanya fasfo dinsu a cikin manyan jakunkunansu a bisa kuskure, don haka bincike domin tabbatar da matsayinsu a na daukar lokaci”.