Maniyyata sun bukaci a dawo musu da kudadensu saboda karin kuɗin kujera

An buƙaci maniyyatan bana da su yi gaggawar biyan N1,918,032.91 ƙari a kan kuɗin kujerar Hajjin bana.

Maniyyata sun bukaci a dawo musu da kudadensu saboda karin kuɗin kujera

Mahajjata a filin Mina

Wasu daga cikin maniyyatan Najeriya sun bukaci Hukumar Alhazai ta Kasa NAHCON da ta mayar musu da kudadensu na aikin hajjin da suka biya.

Hakan ya biyo bayan karin kusan naira miliyan biyu da aka yi musu na tafiya kasa mai tsarki domin sauke farali a bana.

Wannan na zuwa ne bayan da kungiyoyin gamayyar kungiyoyin farar hula na kasar, suka yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya ceto maniyyatan kasar, la’akari da halin matsin tattalin arzikin da ake ciki.

A ranar Lahadi ne, NAHCON ta sanar da cewa an kara sama da naira miliyan daya da dubu 900 na kudin aikin hajjin bana ga maniyyatan da ke shirin tafiya kasar Saudiyya sauke farali, saboda matsalar karyewar darajar kudin kasar.

Darajar kudin Najeriya ta fuskanci koma baya a kan farashin dala a ‘yan kwanakin nan, kodayake a halin yanzu an fara ganin farfadowar darajar kudin kasar, sakamakon matakin da babban bankin CBN ya ce ya fara dauka na shawo kan matsalar.

A ranar 29 ga Maris ne, NAHCON ta ce, za ta rufe karbar kudin maniyyata, kamar yadda mai magana da yawun hukumar, Fatima Sanda Usara ta tabbatar a wata sanarwa.

Binciken da Aminiya ta yi daga Arewaci zuwa Kudancin kasar ya tabbatar da cewa, kalilan na maniyyata ne suka shirya biyan karin kudin da aka musu.

Sai dai kuma da dama daga cikin maniyyatan sun soma hawa kujerar naki, tare da neman hukumomin jin dadin alhazan jihohinsu su mayar musu da kudadensu.

A ranar Lahadin da ta gabata ce NAHCON ta buƙaci maniyyatan bana da su yi gaggawar biyan N1,918,032.91 ƙari a kan kuɗin kujerar Hajjin bana.

Hukumar wadda ta ce yanzu kuɗin sun koma naira miliyan shida da dubu 800 duk kujera ɗaya, ta ce hakan ya faru ne sakamakon tashin farashin dala wadda da ita ce ake yin kiyasin dukkanin abubuwan da maniyyata suke bukata.

Hukumar ta buƙaci maniyyatan da ke son sauke farali a bana kuma suka riga da bayar da kuɗin ajiya da su gaggauta cika kuɗin daga yanzu zuwa ƙarfe 11:59 na daren 28 ga Maris, 2024.

Wannan dai na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar alhazan, Farima Sanda Usara ta fitar a Yammacin ranar Lahadin, tana mai cewa saboda lokacin da aka fitar da farashin kujerar aikin Hajjin bana dala ba ta yi tashin da ta yi ba yanzu.

Hajiya Usara ta ce hukumar za ta rufe karɓar cikon kuɗin ne a ranar 29 ga watan Maris, kuma daga wannan lokaci babu wani maniyyaci da za su saurara matuƙar bai biya kuɗin kafin lokacin ba.

“Wadanda suka kasa biya suna da zaɓi biyu ko dai su rubuta a mayar masu da kuɗinsu ko kuma su ajiye kudin har zuwa shekara mai zuwa.”

Hukumar ta ce mutum 49,000 ne suka biya kuɗin kujerun a farashin baya daga cikin kujeru 75,000 da Saudiya ta ba mahajjan gwamnati yayin da ’yan kasuwa ke da kujera 20,000 wato masu tafiya ta jirgin yawo.

Saboda haka sanarwar ta ce sabbin waɗanda suke da sha’awar sayen kujerar daga jihohin Adamawa, Borno da Yobe, za su biya Naira miliyan 8,225,467.74 yayin da waɗanda suka fito daga sauran yankunan Arewa za su biya Naira 8,254,464.74.

Haka kuma, sabbin waɗanda ke da sha’awar sauke faralin da suka fito daga yankunan Kudu, za su biya Naira miliyan 8,454,464.74, kuma duk a tsukukun wa’adin rufe karɓar kuɗin da Hukumar NAHCON ta bayar.

Ana iya tuna cewa, tun a watan Fabarairun da ya gabata ne hukumar alhazan ta ƙayyade kusan naira miliyan biyar a matsayin kuɗin kuejrar hajjin bana.

Sai dai tun bayan lokacin, hukumar ta soma tababar ƙara wa maniyyatan kuɗi a dalilin tsadar Dala da ke neman hana yi wa maniyyatan dawainiyar da aka saba yi musu ta masauki, abinci da makamantansu.

A wancan lokacin dai, NAHCON ta buƙaci maniyyata daga jihohin Kudancin Najeriya su biya naira miliyan 4,899,000, yayin da maniyyatan Arewa za su biya naira miliyan 4,699,000.

Sai kuma maniyyatan jihohin Yobe da Maiduguri da aka ƙayyade kuɗin kujerarsu a kan naira miliyan 4,679,000.

Dole talauci ya yi katutu a Arewa!

Hauhawar farashin kayayyaki ta ƙaru da kaso 33 a Najeriya — NBS

Kotun Ƙoli ta yi watsi da buƙatar rushe Hukumar EFCC

HOTUNA: Jana’izar tsohon Babban Hafsan Sojin Ƙasa Lagbaja