Maniyyatan bana miliyan ɗaya sun isa Saudiyya
NAHCON ta ce maniyyatan Nijeriya 40,696 sun isa kasa mai tsari.
Hukumomi a Ƙasar Saudiyya sun bayyana cewa kusan maniyyata miliyan ɗaya daga ƙasashe daban-daban ne suka isa ƙasar don aikin Hajjin bana.
Rahoton da kafar sadarwa ta Saudi Gazette ta fitar ya bayyana cewa, ya zuwa ranar Lahadin da ta gabata, adadin maniyyata 935,966 ta dukkan tashoshin jiragen sama da na ƙasa da na ruwa ne suka isa ƙasar.
- A soma duban watan Zhul Hijjah ranar Alhamis — Saudiyya
- Kotu ta yi umarnin isar da sammaci ga Ganduje ta hanyar sadarwa
Ana iya tuna cewa sama da mutum miliyan biyu ne suka biya kudin aikin Hajjin bana, inda daga ciki ake sa ran ‘yan Najeriya 65,000 za su sauke farali.
Tuni dai Hukumar Alhazai ta Nijeriya NAHCON ta ce ta kwashi maniyyatan kasar 40,696 daga cikin jimillar jirage 96 da suka yi jigila.
Rahoton ya ruwaito cewa, Hukumar Da ke kula da fasfot ƙarƙashi babban daraktan da ke kula da fasfot (Jawazat) na cewa mafi yawan mahajjata sun zo ta jirgin sama kuma adadinsu ya kai 896,287, yayin da adadin da suka isa ta hanyoyin ƙasa ya kai 37,280, sai kuma maniyyata 2,399 da suka shiga ƙasar ta tashoshin jiragen ruwa.
Hukumar ta bayyana cewa, tana duk mai yiyuwa wajen sauƙaƙa hanyoyin shiga ƙasar ga baƙi da ikon Allah ta hanyar tallafa wa hanyoyin sadarwarta ta yanar gizo a jiragen sama da na ƙasa da na ruwa da na’urorin fasaha na zamani da ƙwararrun ‘yan ƙasar Saudiyya da suka ƙware a harsuna daban-daban da ke amfani da su ga alhazai.