Maniyyatan Barno da Yobe na fuskantar halin rashin tabbas

Maniyyata aikin Hajjin bana daga jihohin Borno da Yobe  sun fara nuna damuwa kan ko za su samu tashi daga filin jirgin saman Maiduguri don gudanar da aikin Hajjin bana, ko a’a. Galibin wadanda suka zanta da Aminiya a shekaranjiya Laraba, sun bayyana rashin gamsuwa kan abin da suka kira tafiyar “hawayina’’ da shirye-shiryen da […]

Maniyyatan Barno da Yobe na fuskantar halin rashin tabbas
Maniyyatan Barno da Yobe na fuskantar halin rashin tabbas

Maniyyata aikin Hajjin bana daga jihohin Borno da Yobe  sun fara nuna damuwa kan ko za su samu tashi daga filin jirgin saman Maiduguri don gudanar da aikin Hajjin bana, ko a’a.
Galibin wadanda suka zanta da Aminiya a shekaranjiya Laraba, sun bayyana rashin gamsuwa kan abin da suka kira tafiyar “hawayina’’ da shirye-shiryen da suka kamata a kammala da kuma rashin bayyana musu ranar tashi, inda suka ce sabanin takwarorinsu na wasu jihohin da suka samu irin wannan bayanai a kan lokaci. Har ila yau, wasu maniyyatan Jihar Borno sun ce, “Wannan ya sa mun fara samun shakku a zukatanmu kan ko za mu samu damar sauke farali ko a’a.”
A watan azumin Ramadan da ya wuce ne Gwamnatin Tarayya ta ba da umarnin rufe filin jirgin saman Maiduguri, a lokacin da dimbin masu zuwa aikin Umarah suke dakon tashi zuwa Saudiyya.
Da wakilinmu ya tuntubi Hukumar Hajji ta kasa (NAHCON) kan wannan batun ta ce dalilan tsaro ne suka haddasa tsaikon, wanda kuma ba ta hurumin magana a kai.
dimbin maniyyata da suka hada da wadanda gwamnatin Jihar Barno ta dauki nauyi, suka kasance a hedkwatar hukumar da ke hanyar Damaturu, a wani yunkuri na neman bayanai daga hukumomi.