Maniyyatan da za su je Hajji a jirgin farko sun yi hatsari
Motar maniyyatan ta yi hatsari ne a ranar Laraba a kan hanyarsu ta zuwa Abuja inda za su hau jirgin farko a ranar Alhamis.

Maniyyatan aikin Hajjin bana daga Jihar Nasarawa da ke shirin tafiya a jirgin farko sun yi hatsari.
Rahotanni sun nuna mutum hudu sun samu rauni bayan motar maniyyatan ta yi adungure da su ne a ranar Laraba a kan hanyarsu ta zuwa Abuja inda za su hau farko a ranar Alhamis.
- Wa zai biya diyyar rayuka da dukiya da aka rasa a Najeriya?
- Rancen Paris Club: Gwamnati za ta dawo wa jihohi kudadensu
Hatsarin da ya ritsa da bas mai daukar mutum 18 da suke ciki ne a yankin Kara da ke Karamar Hukumar Keffi a Jihar Nasarawa.