Maniyyatan Falasdinu za su fara tashi daga Isra’ila
Hukumonin kasar Isra’ila sun bayyana cewa a karon farko maniyyata Falasdinawa za su fara tashi daga kasar ta jirgin sama don isa birnin Jeddah na kasar Saudiyya, domin sauke farali a aikin hajjin bana.Kamar yadda jaridar Haaretz ruwaito, sawun farko na maniyyatan zai kunshi mutum 766 ne, wanda kamfanin sifurin jiragen sama na Isra’ila mai […]
Hukumonin kasar Isra’ila sun bayyana cewa a karon farko maniyyata Falasdinawa za su fara tashi daga kasar ta jirgin sama don isa birnin Jeddah na kasar Saudiyya, domin sauke farali a aikin hajjin bana.
Kamar yadda jaridar Haaretz ruwaito, sawun farko na maniyyatan zai kunshi mutum 766 ne, wanda kamfanin sifurin jiragen sama na Isra’ila mai suna Milad Abiation zai gudanar, a karshen wannan watan.
A baya dai Falasdinawa wadanda za su sauke farali suna tafiya ne ta mota don isa kasar Jordan, inda suke yada zango na dan wani lokaci kafin su karbi fasfo din kasar wanda zai ba su izinin shiga Saudiyya. Har ila yau, bayan kammala aikin hajjin, sai sun biyo ta Jordan don dawo da fasfo din da aka ba su, kafin su karasa gida ta mota.
Shugaban kamfanin Milad Abiation din ya ce, “an kwashe kimanin shekara uku ana tattaunawa tsakanin kasar Jordan da Isra’ila kafin kammala shirya wannan tafiyar a karon farko a tarihi. A lokacin da ake shirye-shiryen na je kasar Jordan fiye da sau 100, kafin samun amincewar hakan,”inji shi.
Sai dai kuma a ranar Talatar da ta gabata ne, jaridar Arab News ta ruwaito cewa Hukumar da ke Kula da Sifurin Jiragen Saman kasar Saudiyya (GACA), ta musanta labarin. Kuma ta ce ba daya daga cikin filayen jiragen saman kasar da zai gudanar da aikin jigilar. Kakakin hukumar Khaled al-Khaibari ya ce babu wannan shirin. Kuma za a yi jigilar maniyyatan Falasdinawa ne kamar yadda aka saba, wato daga kasar Jordan. Ko kuma maniyyatan su shigo mota kai-tsaye daga kasar Isra’ila zuwa birnin Makkah, ko kuma Madinah.
Akwai dai kimanin maniyyata fiye da miliyan daya da dubu dari uku daga kasashen duniya da za su gudanar da aikin hajjin bana, wanda za a gudanar a cikin watan gobe.