Maniyyatan Filato 135 Ba Za Su Samu Sauke Farali Ba
Maniyyata aikin Hajji guda 135 daga Jihar Filato ba za su samu damar tafiya kasar Saudiyya domin sauke farali a wannan shekarar ba. Wannan ya biyo bayan kasa bada cikon karin kudin da Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta yi a watan Maris na kusan Naira miliyan biyu, wanda ya kai kudin aikin hajji bana […]
Maniyyata aikin Hajji guda 135 daga Jihar Filato ba za su samu damar tafiya kasar Saudiyya domin sauke farali a wannan shekarar ba.
Wannan ya biyo bayan kasa bada cikon karin kudin da Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta yi a watan Maris na kusan Naira miliyan biyu, wanda ya kai kudin aikin hajji bana Naira Miliyan Shida da Dubu Dari Takwas .
Maniyyata daga Jihar Filato sun je ofishin hukumar ne a ranar Juma’a da ta gabata domin biyan cikon kudin da aka kara, sai dai basu samu kowa a ofishin ba.
Jami’in yada labarai na hukumar, Yasir Isma’il, a wata tattaunawa da wakilinmu, ya ce wadanda abin ya shafa ba su iya biyan cikon bane saboda karewar wa’adin.
- NAJERIYA A YAU: Albashin Da Ya Kamata A Riƙa Biyan Ma’aikaci A Wannan Yanayi
- Ma’aikatan wutar lantarki sun nemi a janye ƙarin kuɗin wuta
Ya ce tuni NAHCON ta kammala zayyana sunayen wadanda za su halarci aikin Hajjin bana daga Jihar Filato.
Yasir ya bayyana cewa tun da farko ma da kudin kujerar aikin hajji ke Miliyan Hudu da Dubu Dari Tara, sai da suka ranto Naira Biliyan Biyu daga Gwamnatin Jihar domin kar su rasa adadin kujerun da aka warewa jihar.
“Maniyyata da dama sun kasa biyan kudin aikin hajjin tun yana Naira miliyan 4.9 har zuwa wa’adin da NAHCON ta bayar, sai da muka nemi lamunin Naira Biliyan Biyu don kar mu rasa gurbin da aka ware mana”.
“Mun samu damar biyan kujerun kujeru 1,345 da aka ware wa jihar, amma abin takaici, da wannan batun karin ya taso, hukumar ta iya biyan kujeru 1,210 don baiwa mahajjatan mu damar biya cikin sauki ko da bayan wa’adin da NAHCON ta sanar ya wuce”.
“Ga wadanda suka zo hukumar da kudi a ranar Juma’a da ta gabata, gaskiya ba za su samu damar tafiya aikin hajji ba bana, kamar yadda NAHCON ta bada umarni”.