Maniyyatan Jihar Kebbi 570 sun tsallake rijiya da baya

Kimanin maniyyata 570 daga Jihar Kebbi ne suka tsallake rijiya da baya, bayan da jirgin da ke dauke da su ya samu matsala a injinsa a lokacin da yake kokarin tashi da su zuwa Saudiyya. Lamarin ya faru ne a lokacin da jirgin na Kamfanin Mad Air, yake yunkurin cirawa sama, amma sai biyu daga […]

Maniyyatan Jihar Kebbi 570 sun tsallake rijiya da baya
Maniyyatan Jihar Kebbi 570 sun tsallake rijiya da baya

Kimanin maniyyata 570 daga Jihar Kebbi ne suka tsallake rijiya da baya, bayan da jirgin da ke dauke da su ya samu matsala a injinsa a lokacin da yake kokarin tashi da su zuwa Saudiyya.
Lamarin ya faru ne a lokacin da jirgin na Kamfanin Mad Air, yake yunkurin cirawa sama, amma sai biyu daga cikin injunansa suka samu matsala, kuma nan take ya juyo ya dawo filin jirgin saman Kebbi domin a duba lafiyarsa. Ganin hakan ta auku ne sai Hukumar Jin Dadin Alhazzai ta Jihar Kebbi ta umurci maniyyatan su sauko daga cikin jirgin domin a duba lafiyarsa.
A lokacin da wakilinmu ya isa filin jirgin domin jin ta bakin ma’aikatan kamfanin jirgin ya tarar da jirgin ya wuce zuwa Kano domin canja masa injunan da suka samu matsala. Maniyyatan da wannan matsala ta shafa sun fito ne daga sassan jihar ciki har da’yan majalisar dokoki 10 da wadansu manyan jami’an gwamnatin Kebbi.
A wata sabuwa kuma jami’an tsaro sun yi awon gaba da Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kebbi, Alhaji Mohammed Umar Tilli bisa ga umarnin da Gwamnan Jihar Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya bayar, sakamakon korafe-korafen da maniyyata suka yi kan cacewar kudin guzurinsu.
Jami’an tsaron sun yi awon gaba da shugaban ne tare da sauran jami’an kuma Kakakin Kwamitin Aikin Hajjin Bana na jihar, Mallam Isah Assalafi, ya tabbatar wa wakilinmu aukuwar lamari, inda ya ce hakan ya biyo bayan umurnin da Gwamnan ya bayar ne saboda korafe-korafen da wasu maniyyata da dama suka yi na zargin an rage musu kudin guzurinsu.
A kananan hukumomin Shanga da Arewa ana zargin shugabannin kananan hukumomin da suka sauka da wawure sama da Naira miliyan 50 na kudin maniyyatan, inda a sanadiyar haka ba za su je aikin Hajjin bana ba. Shugaban Kwamitin Aikin Hajji mai kula da Shiyyar Kebbi ta Arewa Alhaji Abubakar Musa danmalikin Kebbi shi ne ya shaida wa wakilinmu haka a filin jirgin saman Birnin Kebbi.
Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin shugabannin kananan hukumomin biyu Alhaji Shehu Mohammed Na-Tsohi da Alhaji Ahmed Y. Tanko amma bai samu nasara ba.