Maniyyatan Kaduna za su cika kudin kujerar Hajji cikin wata 2

Manniyyatan aikin Hajji daga Jihar Kaduna za su biya kafin alkalamin Naira miliyan 2.5, sannan su biya cikon miliyan biyu kafin karshen watan Disamba

Maniyyatan Kaduna za su cika kudin kujerar Hajji cikin wata 2

Maniyatta aikin hajji

Hukumar Jin Dalin Alhazai ta Jihar Kaduna ta ba wa maniyyatanta wa’adin ranar 30 ga watan Disamba 2023 su kammala biyan cikon kudin kujerar aikin Hajji mai zuwa.

Hukumar ta umarci maniyyatan su biya Naira miliyan 2.5 a matsayin kafin alkalami, sannan su biya cikon Naira miliyan biyu kafin cikar wa’adin.

Ta bayyana cewa za ta ba da fifiko da maniyyatan da ba su taba sauke farali ba wajen yin rajista, amma ba za ta amince da biyan kudin kujerar a bisa wakilci ba.

Duk wanda aka maye gurbinsa a kujerar aikin Hajjin da ya biya kuma, to ba za a dawo masa da kudinsa ba, zai an kammala dawo da alhazai daga Kasa Mai Tsarki.

Ta ce daukar matakin ya zama dole saboda yada wasu ke biyan kudin kujerar ba da niyyar su tafi ba, sai don daga baya su sayar wa wadanda ba su samu ba da tsananin tsada.

Hukumar ta ce duk wanda ta gano ya yi haka to ba za ta amince ta maye gurbinsa ba, inda ta garagadi maniyyata su guji biyan kudi ta hannun jami’anta, su biya kai tsaye a banki sannan su kai takardar shaidar biyan kudinsu ga jami’an Hajji da ke kula da kananan hukumominsu.

Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta sanya Naira miliyan 4.5 a matsayin kudin kujerar aikin Hajjin na 2024.