‘Maniyyatan Kano 156 sun sayi kujerun Aikin Hajji na bogi’

Ana zargin tsohon Shugaban hukumar ne ya sayar da kujerun na bogi

‘Maniyyatan Kano 156 sun sayi kujerun Aikin Hajji na bogi’

Kimanin maniyyata 156 da suka fito daga Jihar Kano ne ba za su sami tafiya kasar Saudiyya don sauke farali a Aikin Hajjin bana ba, sakamakon sayar musu da kujerun bogi.

Ana dai zargin tsohon Shugaban Hukumar Jin dadin Alhazan Jihar, Abba Dambatta ya yi.

Wani maniyyaci da ya nemi a boye sunansa, ya bayyana cewa ya biya kudin kujeru biyu, da nasa da na mahaifiyarsa amma daga baya sai aka kira shi aka ce ba za su sami tafiya a bana ba

“A gaskiya ba mu ji dadin hakan ba domin duk mun riga a mun sa rai da tafiyar amma  ga yadda abu ya kasance. Tun farko mai ya sa za su karbi kudinmu sun san cewa ya zarce adadin abin da Hukumar NAHCON ta ba su.”

Ita ma wata maniyyaciya da Aminiya ta tattauna da ita ta bayyana damuwarta game da yadda lamarin ya kasance.

Ta ce, “Lokacin da za mu biya kudinmu sai da muka je muka tambayi hukumar suka ba mu tabbacin cewa akwai kujeru a kasa don haka muka sa rai har muka rika zuwa bitar da ake yi wa alhazai Sai kuma kwatsam aka shaida mana cewa wai mu yi hakuri babu kujerun da za mu tafi. Ba a kyauta mana ba wallahi,” in ji ta.

Amma ta ce, “Mun ji dadin yadda Shugaban Hukumar Jin dadin Alhazan Kano ya yi mana alkawarin cewa badi da mu za a fara tashi Insha Allah amma muna rokonsa da kada a kara mana kudi. Domin Hakan ta faru ga alhazan bara da ba su sami tafiya ba amma da aka zo tafiya bana sai da suka cika kudi. Bayan ba laifinsu ba ne. Idan za a yi adalci bai kamata a kara musu kudi ba.”

A yanzu haka dai Gwamnatin Jihar Kano ta sha alwashin gurfanar da duk masu hannu cikin badakalar sayar da kujerun bogi ga maniyyatan.

Darakta Janar na Hukumar Jin dadin Alhazan Jihar Kano, Alhaji Laminu Danbappa ne ya bayyana haka yayin da yake tattaunawa da manema labarai a Kano.

Alhaji Lamin ya ce shugabancin hukumar karkashin jagorancin Alhaji Abba Dambatta ya sayar da kujeru fiye da wadanda Hukumar NAHCON ta ba Jihar.

A cewarsa, “Na zo na sami Hukumar nan ba a bar min kujerar ko guda daya ba. Haka kuma na tarar sun sayar da kujerun fiye da wadanda Hukumar NAHCON ta ba jihar. A ka’ida Hukumar NAHCON ta ba Jihar Kano kujerun 6,144 amma sai suka sayar da 6,300.

“Bai kamata ka sayar da abin da ba ka da shi ba. Wannan kuskure ne. Ni duk tsawon zamana a wannan Hukumar ban taba sayar da kujerun da ba ni da su a hannuna ba. Ni ina tsayawa a kan iyakar kujerun da NAHCON ta ba ni. ”

Alhaji Lamin Danbappa ya ce wannan ne ya janyo hukumar ta sami matsala a bara yadda aka bar alhazai sama da 700 a kasa ba tare da sun tafi kasa mai tsarki ba.

Sai dai duk kokarin Aminiya ta jin ta bakin tsohon Shugaban Hukumar akan wannan magana ya ci tura inda ya ja bakinsa ya tsuke.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan