Manjo Galma ga Buhari: Kada ka sake fitowa takara

Wani tsohon soja mai suna Manjo Mohammed Bashir Shu’aibu Galma ya bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya yi watsi da masu kiran ya sake tsayawa takara a zaben shekarar 2019, tare da yin koyi da marigayi tsohon Shugaban kasar Afirka ta Kudu Nelson Mandela na kin fitowa takara karo na biyu. Manjo Mohammed Shu’aibu Galma ya […]

Manjo Galma ga Buhari: Kada ka sake fitowa takara

Wani tsohon soja mai suna Manjo Mohammed Bashir Shu’aibu Galma ya bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya yi watsi da masu kiran ya sake tsayawa takara a zaben shekarar 2019, tare da yin koyi da marigayi tsohon Shugaban kasar Afirka ta Kudu Nelson Mandela na kin fitowa takara karo na biyu.

Manjo Mohammed Shu’aibu Galma ya bayyana haka ne sakamakon kiraye -kirayen da wadansu suke yi na Shugaba Buhari ya sake tsayawa takarar a zaben shekarar 2019.

Manjo Bashir Shu’aibu Galma, ya bayar da shawarar ce lokacin da yake tattaunwa da Aminiya, inda ya ce ganin cewar Shugaba Buhari dattijo ne, kuma ya taba rike mukamin Shugaban kasa na soja, kuma shekarunsa sun ja, rashin tsayawarsa takara a karo na biyu zai kara masa martaba da mutunci a idon duniya kamar yadda marigayi Nelson Mandela ya samu.

Manjo Galma wanda yana daya daga cikin mambobin Cibiyar Buhari ta kasa, ya ce, Shugaba Buhari kusan ya cika alkawuran da ya daukar wa ’yan Najeriya lokacin yakin neman zabe, don haka kamata ya yi ya nuna dattaku ya ki fitowa takarar kamar yadda wadansu ’yan siyasa suke ta kiraye-kirayen ya yi.

Ya ce, Shugaba Buhari ya yi alkawarin samar da tsaro da yakar cin hanci da rashawa da ya zamo ruwan dare a kasar nan kuma ya ci nasara, ya yi alkawarin daidaita al’amuran tattalin arzikin kasa kuma ya cika, kuma hakan ya janyo masu yabo hatta daga kasashen waje.

Manjo Galma ya kuma shawarci Shugaban kasar da ya yi tankade-da-rairaya ga ministocinsa, musamman ministocin da ba su taka rawar a-zo-a-gani wajen gudanar da ayyukan ma’aikatunsu kuma ya rage wa wasu nauyin da ya dora musu ta hanyar raba ma’aikatunsu.