Manoma 2009 da suka amfana da APPEALS za su bunkasa nomansu a Kano
Kimanin manoma 2009 ne suka samu tallafin Bankin Duniya da Gwamnatin Tarayya da Gwamantin Jihar Kano inda za su yi amfani da shi don bunkasa harkar kasuwaninsu na noma. Manajan Aikace-Aikace na Kungiyar Inganta Noma don Riba ta Kasa (APPEALS), Dokta Salisu Garba ya bayyana haka ga manema labarai lokacin da ake gudanar da tantancewar […]
Kimanin manoma 2009 ne suka samu tallafin Bankin Duniya da Gwamnatin Tarayya da Gwamantin Jihar Kano inda za su yi amfani da shi don bunkasa harkar kasuwaninsu na noma.
Manajan Aikace-Aikace na Kungiyar Inganta Noma don Riba ta Kasa (APPEALS), Dokta Salisu Garba ya bayyana haka ga manema labarai lokacin da ake gudanar da tantancewar .
Dokta Salisu Garba ya bayyana cewa an tsaara tallafin ne don tallafa wa mata da matasa don su bunkasa kasuwancinsu na noma.
Ya kara da cewa bayan an kammala tantancewar wadanda suka yi nasarar za su samu horo don kara bunkasa iliminsu kan duk wani fannin noma da suka zaba.
A cewarsa, an tanadi duk wasu tsare-tsare wajen bibiya don tabbatar da samun nasarar shirin.
Shi ma Ko’odinetan shirin a Jihar Kano, Hassan Ibrahim ya bayyana cewa an bullo da shirin bayar da tallafin ne don tallafa wa mata da matasa su samu sana’a a harkar noma yadda za su bayar da gudunmawa wajen ci gaban tattalin arzikin kasa.
Da yake jawabi a madadin Gwamnatin Jihar Kano Babban Sakatare a Ma’aikatar Gona Dokta Hadi Bala Yahaya, ya bayyana cewa gwamnati da gaske take game da shirin don ganin matasan da ba su da aikin yi sun samu abin yi domin su bayar da tasu gudunmawar wajen ci gaban kasa.
Dokta Hadi Bala, ya kara da cewa gwamnati ta dauki dukkan matakan da suka kamata don dorewar shirin.