Manoma 6, 670 sun amfana da tallafin Gwamnatin Tarayya a Filato
Mamonan shinkafa akalla 6,670 ’yan asalin Jihar Filato ne suka amfana da shirin Gwamnatin Tarayya a karkashin Babban Bankin Najeriya (CBN). Shirin wanda ake kira cikin Ingilishi da Anchor Borrowers, shiri ne da Gwamnatin Tarayya ta fito da shi don taimaka wa manoma da bashi don a samu bunkasar noma a Najeriya. Kayayyakin aikin gonar […]
Mamonan shinkafa akalla 6,670 ’yan asalin Jihar Filato ne suka amfana da shirin Gwamnatin Tarayya a karkashin Babban Bankin Najeriya (CBN).
Shirin wanda ake kira cikin Ingilishi da Anchor Borrowers, shiri ne da Gwamnatin Tarayya ta fito da shi don taimaka wa manoma da bashi don a samu bunkasar noma a Najeriya.
Kayayyakin aikin gonar da manoman Jihar Filato suka samu sun hada da takin zamani da maganin kashe kwari da maganin kashe ciyawa da injunan ban ruwa da irin shinkafa da sauransu.
An yi rabon kayayyakin ne a harabar Hukumar Bunkasa Harkokin Noma ta Jihar Filato (PADP).
A yayin da ake rabon kayayyakin wanda aka shafe mako uku ana yi, Shugaban kungiyar Manoman Shinkafa ta Jihar Filato, Mista Daudu Aku ya ce manoman sun samu tallafin kayayyakin aikin gona ne bayan cika fom din kungiyar da kuma wani fom mai dauke da adireshinsu da banki ya ba su, bayan kuma hukumomin gwamnati a karkashin Babban Bankin Najeriya da Ma’aikatar Gona ta Tarayya sun tantance su.
Mista Aku ya ce an yi rabon kayayyakin ne a lokaci guda a harabar Hukumar Bunkasa Harkokin Noma ta Jihar Filato (PADP) da ke garin Jos da Mangu da kuma Shendam.
“Daga farko mun tura sunayen ma’aikata dubu tara ne, amma kwamitin tantancewa ya amince da ba da tallafin ga mutum 6,670, kuma monaman da suka amfana an zakulo su ne daga kananan hukumomi 17 na Jihar Filato,” Inji shi.
Ya ce, an kawo tirela 36 na takin zamani zuwa jihar, inda kowace tirela take dauke da buhun taki 600, an kuma kawo injunan ban-ruwa 6,670, wanda ya nuna kowane manomi da aka tantance ya samu injin ban-ruwa daya.
“A cikin tirela 36 aka kawo Jihar Filato an tura tirela 11 ga Arewacin Jihar, takwas zuwa yankin Tsakiyar Jihar, sai kuma tirela 17 ga Yankin Kudancin Jihar.
Hafsat Usman Salami daga Mazabar Naraguta da ke karamar Hukumar Jos ta Arewa, tana daya daga cikin manoman da suka amfana inda take noma rabin hekta, ta kuma bayyana jin dadinta bisa ga tallafin da Gwamnatin Tarayya ta ba manoman jihar.
Ta ce, “An ba ni injin ban-ruwa mai inci uku guda daya da bututun ban-ruwa 10 da iri mai nauyin kilo daya guda 15 da takin zamani na noman shinkafa buhu uku da maganin kashe kwari roba daya da maganin kashe ciyawa roba uku.
Ta ce wannan tallafin zai taimake ta wajen bunkasa noman da take yi, har ta kai ga za ta dogara da kanta, tunda rashin kayayyakin aiki ne ya kawo mata tarnaki wajen noman.
Jonathan Nimdul daga Mazabar Lamingo da ke karamar Hukumar Jos ta Arewa ya bayyana cewa girman gonarsa ya kai hekta daya, dalilin da ya sa aka ba shi injin ban-ruwa mai inci uku da bututun bayi 10 da hos guda 15 da irin shinkafa mai nauyin kilo daya guda 30.
Ya bayyana sauran kayayyakin da aka ba shi da cewa sun hada da takin zamani don noman shinkafa buhu shida da maganin kashe kwari roba biyu da maganin kashe ciyawa roba shida da sauransu.