Manoma dubu 2 daga Jihar Borno sun yi kaura zuwa Yobe
Kungiyar Manoma ta Yankin Arewa maso Gabas, NECAS, ta ce manoma dubu 2 ‘yan asalin Jihar Borno rukuni-rukuni sun yi kaura zuwa Jihar Yobe mai makwabtaka da ita da zummar samun ingantaccen amfanin gona, a yankin na Arewa maso Gabas. Shugaban NECAS na kasa, Alhaji Sadiq Umar Jaware, shi ya bayyana haka, yayin Kaddamar da […]
Kungiyar Manoma ta Yankin Arewa maso Gabas, NECAS, ta ce manoma dubu 2 ‘yan asalin Jihar Borno rukuni-rukuni sun yi kaura zuwa Jihar Yobe mai makwabtaka da ita da zummar samun ingantaccen amfanin gona, a yankin na Arewa maso Gabas.
Shugaban NECAS na kasa, Alhaji Sadiq Umar Jaware, shi ya bayyana haka, yayin Kaddamar da raba taraktocin noma 100 ga manoma a Kananan Hukumomin Jihar, 17.
Shugaban NECAS din, wanda Sakataren Kungiyar, Ahmed Muhammed Dukku, ya wakilta, ya nunar da cewa wannan karamcin, an yi shi ne da niyyar bai wa manoman da aka raba da muhallansu, damar noma a gonakan Jihar Yoben, dan samun dogaro da kai, tare da wadatar cimaka a yankin.
Sai dai ya nuna rashin jin dadinsa, game da abin da ya kira, barin yankin a baya, da a ka yi, ta fuskar damawa da shi a tsare-tsaren noma na gwamnati wanda hakan ne ya zaburar da su, wajen kafa kungiyar, da nufin havaka noman zamani a yankin.
“Za mu rabar da taraktocin noma 600, a daukacin yankin. Sai dai, bisa la’akari da kamshin dan goman da Jihar Yoben ke da shi ga NECAS, muna kaddamar da raba taraktocin 100, a Jihar, domin inganta noman zamani.” In ji shugaban.
Da yake kaddamar da raba taraktocin, Gwamnan Jihar, Mai Mala Buni, ya shawarci manoman da su rungumi noman zamanin da nufin tada komadar tattalin arzikin jihar wanda ta’addacin Boko Haram ya gurgunta.
A cewar gwamnan, babu kasar da za ta bugi kirjin karanta ya kai tsaiko, har sai ta na iya ciyar da al’ummarta. Sa’annan ya bada tabbacin Gwamnatin Jihar a shirye take da ta kulla kawance da dukkan kungiyoyin gwamnati da na masu zaman kansu wajen bunkasa noma a Jihar.