Manoma dubu 25 za su ci moriyar noman shinkafa a Jigawa –AFAN
kungiyar manoma ta AFAN reshen Jahar Jigawa ta yi wa manoma dubu 17 rijista a fadin jahar, Sakataren kungiyar manoman na jahar Jigawa, Malam Abdulaziz Ringim ne ya shaida wa manema labarai haka a ranar Litinin da ta gabata, ya ce burinsu shi ne su yi wa manoma dubu 25 rijista a fadin jahar mai […]
kungiyar manoma ta AFAN reshen Jahar Jigawa ta yi wa manoma dubu 17 rijista a fadin jahar, Sakataren kungiyar manoman na jahar Jigawa, Malam Abdulaziz Ringim ne ya shaida wa manema labarai haka a ranar Litinin da ta gabata, ya ce burinsu shi ne su yi wa manoma dubu 25 rijista a fadin jahar mai kananan hukumomi 27 da za a yi noman shinkafa a kananan hukumomi 23 a cikin wannan shekarar, in ji shi.
Ya kara da cewar gwamnatin jahar za ta baiwa manoma tallafin kayan aikin noman shinkafa daga kan iri da taki da maganin feshi wadda kowanne manomi zai sami tallafin kayan noma wanda kudinsa ya kai naira dubu 32 a cikin wannan shekarar.
Ya kara da cewar a maganar noman shinkafa yanzu a fadin Najeriya jahar Jigawa ce kan gaba sannan ya ce a yanzu haka an ware kananan hukumomi 23 cikin 27 da jahar ke da su don noman shinkafar a lokacin rani.
Ya kara da cewar karamar Hukumar Hadejia ita ce ta fi yawan manoma kimanin dubu 6 da aka yi wa rijista, za su yi aikin noman na bana, sai karamar Hukumar Auyo mai manoma sama da dubu 4. Sai karamar Hukumar Ringim take mara masu baya da manoma dubu 3 da 500, yayin da sauran kananan hukumomin ke da kasa da haka.
Dan haka ma ya bukaci gwamnatin jahar da ta saki kayan aikin noman tun kafin lokacin domin su shiga hannun manoman akan lokaci, yin hakan zai taimaka wajen samun nasara a aikin noman shinkafar daa za yi anan gaba. Sai kuma ya nuna takaicinsa game da yadda manoman ba sa biyan bashin da gwamnati ta ba su, inda y ace wannan karon ya kamata su ba mara da kunya.