Manoma dubu 900 suka yi rijista da kungiyar AFAN don cigaban noma a Jigawa

kungiyar manoman shinkafa ta kasa reshen Jihar Jigawa AFAN, ta bayyana cewa bisa nasarar da aka samu a jihar a fannin noman shinkafa, inda kimanin matasa 762 suka sami nasarar shiga aikin noman shinkafa da gwamnatin jahar ta bullo da shi da nufin wadata kasar nan da abinci za ta iya ciyar da Najeriya. Shugabanin […]

Manoma dubu 900 suka yi rijista da kungiyar AFAN don cigaban noma a Jigawa

kungiyar manoman shinkafa ta kasa reshen Jihar Jigawa AFAN, ta bayyana cewa bisa nasarar da aka samu a jihar a fannin noman shinkafa, inda kimanin matasa 762 suka sami nasarar shiga aikin noman shinkafa da gwamnatin jahar ta bullo da shi da nufin wadata kasar nan da abinci za ta iya ciyar da Najeriya.

Shugabanin kungiyar manoma na Jahar Jigawa, Alhaji Wada Dayyabu Kafin Hausa da Malam Abdul’aziz Miko Jahun suka bayyana haka a yayin wani taron manema labarai a ranar Juma’ar da ta gabata, inda suka bayyana cewa zuwan gwamnatin Buhari da gwamnatin Alhaji Badaru Abubakar ya taimakawa matasa a jahar ta Jigawa.

Ya ce duk da hasarar da manoman jahar suka yi a wajen noman alkama a cikin shekarar da ta gabata, gwamnatin jahar ta taimakawa manoman jahar wajen biyansu diyya akan hasarar da manoman suka yi na yin noman alkama mai yado.

Ya ce gwamnatin jahar ta biya diyyar naira dubu 135 ga kowane daya daga daukacin manoman alkamar da suka yi hasara a cikin shekarar da ta gabata, kuma gwamnatin jahar ta taimaka wa manoman da iri da taki da injinan ban ruwa a matsayin tallafi garesu.

Sannan sai ya shawarci gwamnatin jahar da ta shigar da ‘ya’yan kungiyar manoma ta kasa wato AFAN a duk wasu ayyuka da gwamnatin jahar za ta yi musamman na aikin gona domin sune suka san manoma kuma sune suka san wadanda suke yin aikin gona a jahar.

Ya ce muddin gwamnati ta ce ba za ta yi amfani da ‘ya’yan kungiyar ba wajen harkokin gona, to babu inda shirin zai kai domin su ne suka san manoma, don haka dole idan ana san ayi nasara sai an hada kai da su, sannan shirin zai kai ga nasara.

Ya kuma tabbatar wa manoma cewar taki yana nan makare a cikin dakunan adana taki a jahar, abin da ya rage shi ne abawa manoma takin, kuma ko yanzu manoma suke bukata za su iya zuwa duk inda taki yake a ajiye su saya akan farashin gwamnati.

Ya kara da cewar sun tanadi taki da magangunan feshi domin sayar wa ‘ya’yan kungiyar manoma a farashi mafi sauki ga daukacin manoman jahar ta Jigawa. Ya ci gaba da cewar yanzu haka sama da manoma dubu 11 na shinkafa ne suka yi rijista da kungiyar AFAN domin cin moriyar shirin.

Yayin da sama da manoma dubu 900 suka yi wa kansu rijista da kungiyar manoman ta AFAN a matakan noma daban-daban, ya kara da cewar idan harkokin noma suka inganta, ko makawa babu jahar Jigawa za ta iya ciyar da Najeriya ta fuskar noman shinkafa kawai.

Ya ce babban burinsu shi ne su ga shinkafa ‘yar Najeriya ta na yin gogayya da shinkafar kasashen waje a fadin duniya baki daya, dan haka ya bukaci gwamnatin tarayya da ta baiwa manoma iri da wuri akan lokaci saboda rashin samun iri akan lokaci yana dakushe harkokin noman baki dayansa.