Manoma miliyan daya za su amfana da shirin Babbar Gona cikin shekara 5
Kimanin manoma miliyan daya ne za su amfana da bashin noma nan da shekara biyar masu zuwa. Darakta Janar na Kungiyar Babbar Gona, Mista Bukola Masha ya bayyana haka lokacin da suka gudanar da taron shekara na tsawon kwana uku tare da Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammad Sanusi II wanda shi ne uban kungiyar. […]
Kimanin manoma miliyan daya ne za su amfana da bashin noma nan da shekara biyar masu zuwa. Darakta Janar na Kungiyar Babbar Gona, Mista Bukola Masha ya bayyana haka lokacin da suka gudanar da taron shekara na tsawon kwana uku tare da Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammad Sanusi II wanda shi ne uban kungiyar.
Mista Masha ya ce zuwa yanzu kungiyarsu ta kashe fiye da Naira biliyan shida wajen tallafa wa kananan manoma dubu 70 a fadin kasar nan.
Darakta Janar din ya ce sun raba bashi na dubu 140 na kayayyakin noma ga manoman masara inda suka shuka kimanin kadada dubu 100 a jihohi biyar na Arewacin Kasar nan da suka hada da Kano da Kaduna da Bauchi da Katsina da Filato.
A cewarsa duk da cewa shirin Babbar Gona ya mayar da hankali kan noman masara amma yana bayar da damarmaki ga sauran kayayyakin amfanin gona da shirin zai tallafawa kimanin manoma miliyan daya zuwa shekarar 2025. “Abin da muka fi mayar da hankali a kai shi ne noman masara sai dai zuwa yanzu muna bayar da damarmaki ga sauran bangarorin don bunkasa shirin. Abin da kawai muke bukata daga wurin manomi shi ne gona da kuma aiki tukuru. Muna bayar da horo a kan dabarun noman zamani da taki da iri da magunguna masu inganci,” inji shi.
A jawabin Darakta a Babbar Gona da ke wakiltar Alhaji Bello Maccido (Wakilin Sakkwato) ya bayyana cewa Babbar Gona ta samu karbuwa a ciki da wajen Najeriya domin niyyarta ta tallafa wa harkar noma wadda ta kara wani kaso a cikin tattalin arzikin kasar nan. “Ko a wannan taro namu na wuni uku mun karbi baki da ke hadin gwiwa da mu daga Bankin kasar Jamus. Baya ga wannan Babbar Gona na samun tallafi daga cibiyoyin hada-hadar kudi na kasashen waje daban-daban. Mun yi tunanin tallafa wa harkar noma ce saboda imanin da muka yi cewa ita ce harkar da ke bunkasa tare da kyautata rayuwar dan Adam, wadda za ta inganta rayuwar manomanmu. Haka harkar noma na bunkasa tattlin arzikin kasa da kashi 29 cikin 100. Kuma ba kamfaninmu kadai ne ke tallafa wa Babbar Gona ba akwai cibiyoyin hada-hadar kudi da suke tallafa wa shirin,” inji shi.
Mafi yawan wadanda suka amfana daga tallafin na Babbar Gona sun nuna jin dadinsu kan shirin inda suka yi fatar dorewarsa.
Malam Halliru Sale wanda ya amfana daga Jihar Kaduna ya ce ya fa’idantu daga horarwar da Babbar Gona ta yi masa a kan dabarun noman zamani . Ya ce “Zan iya cewa kafin zuwan Babbar Gona ba noma muke yi ba hargitsa kasa kawai muke yi, saboda abin da muke girbewa a yanzu ya ninninka na baya.”
Wata wadda ta amfana mai suna Hajara Luka ta ce: “Da farko mun ji dar-dar kan abin da suka zo da shi; amma bayan da muka gwada sai muka ga amfanin abin. A da ina girbe kimanin buhu takwas na masara a rabin kadada, amma a yanzu ina girbe kusan buhu 25 a rabin kadadar.”