Manoma na bukatar ilimin noman zamani – Kwamishina
Kwamishinan Aikin Gona na Jihar Kebbi, Barista Attahiru Maccido ya ce, kashi 80 cikin 100 na manoman jihar kananan manoma ne da ke bukatar ilimin zamani domin inganta harkarsu ta noma. Kwamishinan ya ce noma hanya ce ta yin arziki inda wadansu jama’a suka dauke shi sana’ar wahala. Ya ce, yanzu kasashen waje sun yi […]
Kwamishinan Aikin Gona na Jihar Kebbi, Barista Attahiru Maccido ya ce, kashi 80 cikin 100 na manoman jihar kananan manoma ne da ke bukatar ilimin zamani domin inganta harkarsu ta noma.
Kwamishinan ya ce noma hanya ce ta yin arziki inda wadansu jama’a suka dauke shi sana’ar wahala. Ya ce, yanzu kasashen waje sun yi nisa wajen inganta sana’ar noma daga yadda ake yin sa a shekarun baya zuwa na zamani.
Kwamishinan ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da wakilinmu a ofishinsa a Birnin Kebbi, inda ya shawarci manoman jihar su tashi tsaye wajen yin amfani da kayayyakin zamani domin inganta harkarsu ta noma. “Dole ne manoma su tashi tsaye wajen inganta wannan sana’a tasu, dole ne manomanmu su dauki noma a matsayin sana’a domin ta haka ne za su rika bin duk hanyoyin da suka dace wajen inganta noman,” inji shi.
Ya ce “Kasar Thailand kasa ce da ta shahara wajen noman shinkafa da samar da abinci a duniya amma kuma abin mamaki, kasar ba ta da rabin kasar noma irin wadda Allah ya ba Najeriya. Amma saboda yin amfani da bincike da kimiyya yanzu Thailand tana kan gaba wajen samar da abinci ga kasashen duniya mu ma Jihar Kebbi haka muke son mu zama a kan gaba a cikin kasashen duniya masu alfahari da aikin noma.”
Kwamishinan ya kara da cewa, tun ranar da Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin noma a Jihar Kebbi aikin noma ya farfado saboda ko an mika ragamar aikin noma ga mai kishin kasa da son jama’a su zama masu dogaro da kansu domin samun karin arziki wato mai girma Gwamnan Jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu.
Kwamishinan ya ce, gwamnatin Jihar Kebbi tana kokari wajen taimaka wa manoman jihar da dabarun zamani da za su taimaka musu domin inganta noma a fadin jihar.
Ya ce, ko a kwanakin baya gwamnatin jihar ta rarraba wa manoma kudaden tallafin yin noman rani na shekara 2019, inda manoma 8,600 suka samu Naira bashin Naira dubu 150 kowanensu. Ya ce a shekara uku da suka gabata manoman shinkafa dubu 120 suka amfana da tallafin yin noma, sai manoman waken suya dubu biyar da suka amfana da shirin ba da tallafin noma, manoma alkama manoma dubu 1600 gwamnatin jihar ta ba rancen noman alkama.
Kwanmishinan ya ce gwamnatin jihar ta rarraba wa manoma jihar sama da Naira biliyan 15, inda ya ce, yanzu haka ta sayo taraktocin noma 100 da kananan taraktoci da ake kira Power Tiller guda 80. Kuma ya ce a yanzu suna da taki sama da tan 100 na taki NPK sai tan 100 na Yuriya domin raba wa manoman rani an kuma ware Naira miliyan 300 domin raba wa masu kamun kifi a jihar.
Ya ce gwamnatin jihar ta sayo injunan casar shinkafa guda 150 domin raba wa mata don cashe.