Manoma sun dara bayan samun ruwan sama a Taraba

Akwai wuraren da har kawo yanzu sai dai samun hadari holoƙo.

Manoma sun dara bayan samun ruwan sama a Taraba

marka-marka

Manoma sun dara sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka samu a ranakun Alhamis da Juma’a a Jihar Taraba.

Wannan dai na zuwa ne bayan shafe fiye da makonni huɗu ba tare da samun ruwan sama ba a jihar, lamarin da ya sanya shuke-shuken manoman suka tamushe.

Sai dai bayanai sun ce an samu mamakon ruwan saman da ya kwarara tun daga karfe 7.30 na yammacin ranar Alhamis har zuwa wayewar gari Juma’a.

Samun ruwan saman da aka yi ya karta wa manoman ƙwarin gwiwar tatsar albarkar daminar bana, inda za su sake sabunta shuka amfanin gonar da suka ƙone sanadiyar rashin ruwa.

Aminiya ta ruwaito cewa, an shafe akalla kwanaki 45 ba tare da samun ruwan saman ba a sassa da dama na Jihar Taraba, lamarin da a yanzu saukar ni’imar ta faranta wa manoman.

Amma duk da haka, bincike ya nuna cewa akwai wuraren da har kawo yanzu sai dai samun hadari holoƙo.

Wani manomi a Maihula, Alhaji Maihula ya shaida wa Aminiya cewa, ba su samu ruwan sama sai dai an samu yayyafi na ɗan takaitaccen lokaci a ranar Alhamis.

A cewarsa, an shafe makonni babu ruwan sama a yankin, lamarin da ya janyo a yanzu shuke-shuken da suka yi ke ci gaba da mutuwa.

Amma a ƙananan hukumomin  Jalingo da Gassol da Ardo-Kola da Karim-Lamido da Gashaka, an tafka ruwan saman tamkar da bakin ƙwarya tun da yammacin jiya Alhamis har zuwa wayewar gari Juma’a.

Rahotanni na cewa mazauna jihar sun dukufa wajen gabatar da addu’o’in da azumi domin roƙon Allah Ya kawo musu ɗauki.

Malaman addinai da sarakunan gargajiya na ci gaba da jagorantar al’ummma a masallatai da majami’ai domin samun luɗufi a lamarin.