Manoma sun koka da jabun magungunan feshi a kasuwanni
Manoma da sauran masu amfani da magungunan feshin kwari da na ciyawa a Jihar Kano sun koka bisa yadda jabun magungunan suke neman mamaye kasuwannin jihar, wanda a cewar su hakan babbar barazana ce ga sana’ar su ta noma. Mafiya yawan manoman da wakilinmu ya tattauna da su sun nuna rashin jin dadinsu dangane da […]

Manoma da sauran masu amfani da magungunan feshin kwari da na ciyawa a Jihar Kano sun koka bisa yadda jabun magungunan suke neman mamaye kasuwannin jihar, wanda a cewar su hakan babbar barazana ce ga sana’ar su ta noma.
Mafiya yawan manoman da wakilinmu ya tattauna da su sun nuna rashin jin dadinsu dangane da yadda jabun magungunan suke neman maye gurin masu kyau a kasuwanni da sauran wuraren sayar da kayan aikin gona a fadin jihar, tare da yin godiya ga hukumumin tsaro da hukumomin kula da ingancin kayayyaki bisa yunkurin da suke yi na dakile yawaitar jabun magungunan feshin a cikin kasuwannin jihar.
Wani dan kasuwa mai sana’ar sayar da magungunan feshi, wanda kuma ya bukaci da a sakaya sunan sa ya shaida wa Aminiya cewa gaskiya akwai jabun magunguna a kasuwannin Jihar Kano, sannan akwai ’yan kasuwa masu tarin yawa da suke yin magungunan a gidajensu suna kai wa kasuwanni, amma ana kallon su babu wani mataki da aka dauka a kansu.
Manoman sun sun koka da cewa akwai hukumomi na musamman da suke da alhakin kula da ingancin kayayyaki.
Sannan ya yi bayanin cewa, masu yin jabun magungunan suna canza kamannin kwalaben zuba maganin da kwalayen da kuma lauin su, ta yadda ba za a gane na gasken ba, inda kuma ya sanar da cewa sun kafa wani kwamiti a asirce, domin tona daukacin masu yin jabun magunguna suna shigar da su kasuwannin Jihar Kano.
Binciken da wakilin mu ya gudanar ya ruwaito cewa yanzu haka hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki kan sana’ar sayar da magungunan feshi da kamfanonin sarrafa magungunan sun fara daukar matakai na tsaftace kasuwannin daga matsalar jabun magunguna, tare da yin hukunci ga dukkanin wadanda aka samu da jabun magani a shagunan sa ko wajen ajjiyar kayayyakin sa.