Manoma sun koka kan rashin samun isasshen tallafin noman shinkafa
Jihar Kaduna na daga cikin jihohin da ke noman shinkafa musamman a kananan hukumomin Jama’a da Kaura da Kauru da kuma Jaba wadanda ke kan gaba a noman shinkafa a yankin kudancin jihar. Sai dai yawancin masu noman shinkafar suna korafi, inda daya daga cikinsu ya bayyana wa Aminiya a gonarsa da ke garin Jagindi […]
Jihar Kaduna na daga cikin jihohin da ke noman shinkafa musamman a kananan hukumomin Jama’a da Kaura da Kauru da kuma Jaba wadanda ke kan gaba a noman shinkafa a yankin kudancin jihar.
Sai dai yawancin masu noman shinkafar suna korafi, inda daya daga cikinsu ya bayyana wa Aminiya a gonarsa da ke garin Jagindi Tasha da ke Karamar Hukumar Jama’a, Abdullahi Nda, cewa ba masu noman ne ke cin gajiyar tallafin da gwamnati take bayarwa don noman shinkafar ba.
Abdullahi Nda, wanda ya ce ya taso cikin harkar noman shinkafa, inda ya gada daga daga mahaifinsa ya ce, shekararsa 20 yana noman, inda yake noma akalla hekta goma na shinkafa a kowace shekara. Abdullahi Inda ya ce, jama’a daga jihohin Kaduna da Filato da Nasarawa da Birnin Tarayya Abuja ke zuwa su sayi shinkafa a garin a kowace Alhamis da kasuwar garin ke ci.
Nda, wanda ya ce har yanzu adadin abin da ya saba nomawa shekara uku zuwa hudu bai karu ba saboda rashin tallafi daga gwamnatocin jihohi zuwa na tarayya, ya ce abin da kawai suka samu shi ne bambancin farashi saboda kara daraja da tsadar da ta yi.
Ya ce, yanzu suna sayar da buhun shinkafar da ba a guma an casa ba akan Naira dubu 12 maimakon Naira dubu 6 da suke sayar da shi a shekarar 2015.
“Amma a tsakanin watan shida zuwa watan bakwai mukan sayar da shi har Naira dubu 20. Ka ga bambancin a farashi ne amma da a ce akwai tallafi ya kamata a ce, abin da nake nomawa zuwa yanzu ya fi haka,” inji shi.
Ya jinjina wa gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan kokarin tallafa wa harkar noma da yake yi sai dai ya koka kan yadda tallafin ba ya isa ga manoman asali, wanda ya samu isowa kuma ba ya isarsu.
“Ni da nake bukatar buhu 50 na taki sai aka ba ni buhu uku kacal! Ta yaya zan iya bunkasa harkar? Gaskiya muna bukatar gwamnati ta agaza mana da magungunan feshi da iri mai kyau da taki da kuma rancen kudi marar ruwa domin bunkasa noman shinkafa da muke yi a nan Kudancin Kaduna,” inji shi.