Manoma waken suya dubu 200 suka sami tallafin Anchor Borrowers a bana
Manoma waken suya da masu samar da iraruwan waken suyan tare da kafofin kudade sun hallara a Abuja, a wajen wani taron masu ruwa da tsaki dan fara aiwatar da shirin tallafawa manoma na babban bankin Najeriya wato ‘Anchor Borrowers’ na noman shekarar nan. Farfesa Nafi’u Abdu, wanda shi ne shugaban kungiyar manoman waken suya […]
Manoma waken suya da masu samar da iraruwan waken suyan tare da kafofin kudade sun hallara a Abuja, a wajen wani taron masu ruwa da tsaki dan fara aiwatar da shirin tallafawa manoma na babban bankin Najeriya wato ‘Anchor Borrowers’ na noman shekarar nan.
Farfesa Nafi’u Abdu, wanda shi ne shugaban kungiyar manoman waken suya na kasa, SOFAN, a takaice kuma kwararre a harkar nakaltar iraruwan shuka ya ce a yanzu manoma sun hade waje guda da zummar cin gajiyar bukatar da ake yiwa waken suya ba ma a Najeriya kadai ba, a’a har ma a yankin Asiya da kuma sauran sassa daban-daban na duniya.
Taron ya sami halartar Manajan Gudanarwa na Bankin Manoma, Kabiru Mohammed, da jami’ai daga babban bankin Najeriyar da ma wasu bankunan kasuwanci da kuma masu sarrafa iraruwan shuka da dai sauran masu jibi da harkar.
Ya ce: “A halin yanzu mun yi wa manoma dubu 200 rajista da kungiyar don noman shekarar na da muke ciki ta 2019. Kuma kowanne manomi zai noma akalla zai noma filin da girmansa yakai fadin kadada biyu-hakan nan nufin kadada dubu 400 kenan jimilla, kuma ana hasashen samar da waken suyan da yawansa yakai tan miliyan daya, a lissafin kowanne hekta zai samar da akalla tan biyu da rabi.”
Kwararren jami’in noman wanda ya alkinta shirye-shiryen noma daban daban a ciki da wajen Najeriya-shi ne kashin bayan kafa kungiyar manoman waken suyan, bayan ya yi aikace-aikace da dama akan noman Cowpea a ciki da wajen Najeriya.
Waken suya dai ya kasance daya daga cikin amfanin gonar da ke kamshin dan goma a duniya-kuma ya na daga cikin amfanin gonar da kamfanoni dake matukar bukata da ake nomawa a Najeriya. A na yawan noman waken suyan a galibin jihohin kasar, sakamakon muhimmacinsa da kuma gudummawar da yake bayarwa ta fuskar samar da abinci ga mutane da ma dabbobi.
Najeriya dai ta kasance jagaba ta fuskar noman waken suya a yankin Kudu da Sahara, inda jihohin Benuwai da Nasarawa da Kaduna da Kebbi da Kwara da Jigawa da Katsina da Borno da Kano da Zamfara da Gombe da kuma birnin tarayya Abuja da ma wasu sassan Kudu maso Yamma ke kan gaba wajen nomawa.