Manoma za su dara kan dawowar Kamfanin Tumatir na Dangote
Manoman tumatir sun dade suna fuskantar matsala kan noma da sarrafawa tare da ajiye tumatir. Abin tausayi shi ne yadda manoma a kusan dukan jihohin da ke noma tumatir suke busar da shi ta hanyar shanya shi a gefen titi. Abin bakin cikin shi ne yadda busar da tumatir din ya zama hanya daya tilo […]
Manoman tumatir sun dade suna fuskantar matsala kan noma da sarrafawa tare da ajiye tumatir. Abin tausayi shi ne yadda manoma a kusan dukan jihohin da ke noma tumatir suke busar da shi ta hanyar shanya shi a gefen titi.
Abin bakin cikin shi ne yadda busar da tumatir din ya zama hanya daya tilo ga manoman tumatir din wajen rage asarar da suke gamuwa da ita bayan an yi girbi.
Wani manomin tumatir Malam Usman Dorawar Sallau, ya shaida wa Aminiya cewa, idan noman tumatir zai samu kular da yake bukata daga gwamnati, Najeriya za ta zama babbar kasa da ke noman tumatir a duniya ba wai kawai a Afirka ba.
Ya ce, a cikin shekara biyar da suka gabata gwamnatoci sun yi ta kokarin ganin an rage asarar tumatiri da ake samu bayan lokacin girbi. Sai dai ya bayyana cewa hanya daya wacce take madogara ga rage wannan asara da manoma suke yi ita ce ta fara aiki da Kamfanin Tumatir na Dangote ya yi. “Duk da cewa Najeriya tana shigo da markadadden tumatir daga kasashen waje da ya kai tan dubu 300 wanda hakan ya ke janyowa masu noma tumatir a kasar suke shiga halin ni-’ya-su, bude kamfanin zai rage asarar da ake samu.”
Yanzu haka manoma da dama sun fara nuna farin cikinsu da fara aikin kamfanin na Dangote wanda yake Kadawa a Karamar Hukumar Garun Malam a Jihar Kano, inda suke fatar cewa abin da ya dade yana damunsu zai zo karshe.
A cewar Shugaban Kungiyar Manoman Tumatir ta Kasa, reshen Jihar Kano Alhaji Sani Danladi Yadakwari idan har kamfanin ya fara aiki ya tabbata asarar da manoman suka saba yi za ta ragu ko ta kau musamman da yake a yanzu har an kai ga cimma yarjejeniya kan wasu sharudda wajen fara gudanar da harka a tsakanin kamfanin da kungiyarsu.
Ya kara da cewa, fara aikin kamfanin zai bunkasa harkar noman tumatir wanda a baya manoman tumatir din suka rasa. Ya ce abin takaici ne a ce masu kamfanonin tumatir sun dogara ne kacokan kan shigo da tumatir daga waje, wanda hakan yake barazana ga manoman tumatir a kasar nan.
Da yake bayani game da farashin tumatir din, Alhaji Sani ya ce an samu matsaya a tsakanin Kamfanin Dangote da kungiyarsu kan farashin wanda aka dade ana musayar yawu a kai. “Mun yarda cewa kamfani zai sayi kilo daya na tumatir daidai da farashin da ake sayarwa a kasuwa wannan kuma zai zama abin da zai iya canjawa a duk bayan kwana biyu saboda haka kasuwar gwari ta gada. Ina farin cikin bayyana cewa wannan mataki ne da ya yi mana dadi,” inji shi.
Ya ce, kamfanin yana da wani shiri da zai tabbatar da cewa manoman tumatir sun samu ingantaccen irin sabon nau’in noma na ‘greenhouse’ wanda abu ne da zai taimaka wa manoman.
Da yake jawabi ga manema labarai Manajan Kamfanin Tumatir na Dangote Malam Abdulkarim Kaita ya ce, zuwa yanzu an fara samar da tan 1,200 a kullum.
Ya ce, kamfanin ya yi shiri sosai don ganin an samu nasarar aiki a wannan lokaci.
A cewarsa kamfanin ya samar da miliyoyin ingantaccen iri daga sabon nau’in noma na ‘greenhouse’ wanda za a raba ga manoma. “Kamfani ya samar da wani shiri na ganin an samu kyakkyawar alaka a tsakaninsa da manoman tumatir. Kamfanin ya samar da kadada biyu da rabi na sabon noman ‘green house’ wanda zai rika samar da iri kwaya miliyan 10 duk wata da za a rika raba wa manoman tumatir don taimaka musu,” inji shi.
Ya ce “Mun yi yarjejeniya da masu ruwa-da-tsaki a harka samar da tumatir. mun yarda za mu rika sayen tumatir a kan farashin kasuwa wanda tuni mun fara. Na ji dadin yadda manoman tumatir suke bayar da hadin kai a kan haka.”
Ya ce Kamfanin Tumatir na Dangote zai samar da tumatir mai kyau kasancewar tumatir ne mai inganci. Ya kara da cewa, don kamfanin ya samu nasarar abin da ya sa a gaba wajen samar da markadadden tumatir akwai bukatar shugabanni su tabbatar da cewa, dokar hana shigo da tumatir ta yi aiki sosai
“Gwamnatin Tarayya ta yi abin a zo a gani waje kafa dokar hana shigo da tumatir cikin kasar nan, amma akwai bukatar ta kara kaimi wajen ganin dokar ta yi aiki sosai. Wannan babu shakka abu ne da zai taimaka wa manoman da kamfanin da kuma sauran mutanen kasar nan domin sanin kowa ne sama da kashi 90 na markadadden tumatir din da ake shigowa da shi ba ya da inganci. Kuma duk da an san ba ya da inganci amma har yanzu an bar wadanda suke shigowa da shi suna ci gaba da abin da suke yi. Namu tumatir din mai inganci ne wanda ba ya da wata cutarwa domin yana nan da dandanonsa na asali har zuwa wata 12,” inji shi.