Manoma za su iya amfani da ganyen dogon yaro dan adana amfanin gona – Masani
Wani kwararre a harkar noma ya ce manoma za su iya amfani da ganyen dogon yaro (dalbejiya) wajen ajiya tare da kare hatsi daga kwari masu lalata amfanin gona. Masanin, Mista Fidelis Ozor, wanda Daraktan Ayyuka ne a Ma’aikatar Ayyukan Gona ta Jihar Enugu, ya bayyana haka ne a wata ganawa da ya yi da […]
Wani kwararre a harkar noma ya ce manoma za su iya amfani da ganyen dogon yaro (dalbejiya) wajen ajiya tare da kare hatsi daga kwari masu lalata amfanin gona.
Masanin, Mista Fidelis Ozor, wanda Daraktan Ayyuka ne a Ma’aikatar Ayyukan Gona ta Jihar Enugu, ya bayyana haka ne a wata ganawa da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, (NAN), a Enugu.
Mista Ozor, ya ce maimakon amfani da magunguna masu sinadarai wajen adana amfanin gona, manoma suna iya amfani da busassun ganyen dogon yaron zai taimaka wajen kawar da miyagun kwarin daga lalata hatsin da aka ajiye.
A cewarsa, da zarar an saka busassun ganyen dogon yaron cikin hatsin, to shakka babu za su aikin da magungunan kashe kwarin za su yi, wajen ajiya.
“Ya kamata manoma su kwana da sanin cewa, ana amfani da ganyen dogon yaro wajen ajiya, sakamakon yadda suke da karfin shanye danshin da ke cikin amfanin gona,” inji shi.
Ya ci gaba da cewa, ganyen dogon yaron zai taimaka sosai wajen adana amfanin gona na tsawon watanni ba tare da fargabar kwari su dirar wa hatsin ba.
Daraktan, ya kara da cewa, galibin magungunan kashe kwarin da ake amfani da su wajen kashe kwarin, suna da illar gaske ga lafiyar dan Adam, wanda hakan ke janyo matsalolin lafiya nan da can.