Manoman alkama sun koka da faduwar farashi a Kano
Manoman alkama a Jihar Kano sun nuna damuwarsu a kan rashin ingancin farashin alkamar, suna masu danganta lamarin da wata barazana ga noman alkamar a jihar. Sai dai a wata ganawa da jaridar Daily Trust, a Kano, Shugaban kungiyar gamayyar manoman Najeriya, AFAN, Alhaji Farouk Rabiu Mudi, ya ce kungiyar na neman samar da dabarbarun […]
Manoman alkama a Jihar Kano sun nuna damuwarsu a kan rashin ingancin farashin alkamar, suna masu danganta lamarin da wata barazana ga noman alkamar a jihar.
Sai dai a wata ganawa da jaridar Daily Trust, a Kano, Shugaban kungiyar gamayyar manoman Najeriya, AFAN, Alhaji Farouk Rabiu Mudi, ya ce kungiyar na neman samar da dabarbarun shawo kan wannan matsalar.
A cewarsa: “Bara, daidai wannan lokacin, ana sayar da alkamar a kasuwanni a farashin Naira dubu 18 kowanne buhu-wanda a ganinmu, farashi ne mai dan gwabi. Amma a yanzu da nake Magana da kai, ana sayar da alkamar a kan Naira dubu 14, kowanne buhu. Wannan ai abin kaico ne, da yake da illa ga manoman alkamar a jihar Kano. Sabuwar dabarar da matsakaitan dillalan alkamar, suka fito da ita na sayan amfanin kai tsaye daga hannun manoman, yayi matukar kassara da dama cikin manoman alkamar.” Inji shi.
Ya kuma kara da cewa, kungiyar ta AFAN, na tuntubar wadanda lamarin ya shafa, dan samarwa tufkar hanci. Inda yaci gabada cewa, kungiyar tana kuma tattauna da masu gudanarwar wata cibiyar musayar kayayyakin amfanin gona da ya lashe biliyoyin Naira da ke Gezawa, wanda ba a kai ga kaddamar da shi ba, don yin aiki tare da alkinta dabarbarun da cibiyar ta bullo da su.