Manoman alkama sun ragu sanadin fifita noman shinkafa

Duk da yawan bukatar alkama da ake da ita a Najeriya wadda ta kai tan miliyan 4.2  kuma kudinta ya kai Dalar Amurka biliyan 4.3 a duk shekara, a yanzu ana samun kudin shiga kadan ne a fannin noman alkama. Noman alkaman ya yi kasa daga tan dubu 600 zuwa kasa da tan dubu 400, […]

Manoman alkama sun ragu sanadin fifita noman shinkafa

Alkama

Duk da yawan bukatar alkama da ake da ita a Najeriya wadda ta kai tan miliyan 4.2  kuma kudinta ya kai Dalar Amurka biliyan 4.3 a duk shekara, a yanzu ana samun kudin shiga kadan ne a fannin noman alkama.

Noman alkaman ya yi kasa daga tan dubu 600 zuwa kasa da tan dubu 400, an samu tazara mai yawa kamar yadda masu ruwa-da-tsaki a harkar suka sanar.

Shugaban Kungiyar Manoman Alkama ta Najeriya (WFAN), Alhaji Salim Muhammad ya bayyana wa majiyarmu halin da kasar ke ciki a harkar noman alkama yayin tattaunawar da aka yi da shi.

Shugaban ya ce, babban kalubalen noman alkama shi ne, farashin alkama a kasuwanni. Manyan masu sayan alkama su ne, Kungiyar masu Kamfanonin Sarrafa Fulawa ta Najeriya sun bukaci hukumomi su daidaita farashin alkamar. “Suna kwatanta farashin alkamar da wadda ake shigowa da ita cikin kasar nan da ta cikin gida da ake nomawa. Amma abin da ba a fahimta ba shi ne, kamfanonin Najeriya ba su da isassun kayan aiki da za su taimaka musu wajen kammala abin da suke sarrafawa, don haka za a ga kudin da ake sarrafa kaya ya fi na farashin yadda za a sayi wadda aka shigo da ita daga waje,” inji shi.

Alhaji Salim, ya ce, “Abin da zai ba da mamaki shi ne, lokacin da na san farashin yadda ake sarrafa kayan kamfanoni a kasashen waje irin su Meziko da wasu kasashen Kudancin Amurka, idan za a kwatanta da farashin da Dalar Amurka wajen sarrafa kamfanonin alkama, na Najeriya ya fi yawa. Wannan abin mamaki ne, saboda gwamnatocin suna tallafa musu da kudade don kara musu karfin gwiwa wajen sarrafa abubuwan da za su iya fita da su zuwa kasashen waje.

“Amma a nan Najeriya babu wani tallafi da gwamnati ke bayarwa tun daga fara kafa kamfanoni zuwa lokacin da ake sarrafa abubuwan da kamfanonin za su sayar. To wannan ya rage wa manoman Najeriya su sayi abin da za su sarrafa na gida a kasuwannin kasar a farashin da aka sanya, sannan a karshe abin da aka sarrafa shi zai bayyana farashin da za a sayar a kasuwannin,” in ji Alhaji Salim.

Alhaji Salim ya ce, kalubale na biyu da manoman alkama suke fuskanta a yanzu shi ne ingantaccen irin alkama, saboda yanzu mafi yawan irin alkamar da wadansu manoma ke amfani da shi ba ya samar da yabanya da yawa kuma wannan yana alaka ne da karancin kudin gudanar da binciken daga cibiyoyin noma ta yadda za a iya samun abubuwa da dama na irin da manoma za su shuka akalla a shekara.

“Zan iya cewa tun shekarar 2015 lokacin da Hukumar Tafkin Chadi ta fitar da wasu irin da manoma za su iya shukawa, wadanda har yanzu ana amfani da su, yayin da ake da bukatar wata hanya ta kimiyya akalla sau biyu a shekara kamar yadda wasu kasashen suke yi. Hakan zai bunkasa abin da ake nomawa, idan har ana iya aiwatar da hakan Najeriya za ta iya yin kafada da sauran kasashen waje a harkar noman alkama,” inji Alhaji Salim.

Shugaba ya ce, tun lokacin aka fara shirin karbar rancen aikin gona na Anchor Borrowers na Bankin CBN ne a bana kawai suka fara samun wasu kudade daga kamfanonin da suke sarrafa alkama sakamakon rashin samun wadataccen abin da suke bukata wajen noman alkamar.

A bana akwai manoma dubu 9 zuwa dubu 10 da suka samu tallafin shirin duk da wasu kananan manoma sun mai da hankali wajen noman shinkafa ko masara.

Shugaban Kungiyar ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta yi wani tsari da zai taimaka wajen samar da alkama kamar yadda aka yi wa noman shinkafa.

“Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya  kaddamar da shirin noman shinkafa da alkama a lokaci guda kwanakin baya, amma sai ga shi Gwamnatin Tarayya ta mai da hankali ne wajen noman shinkafa kawai, ba tare da maganar noman alkama ba,” inji shi.