‘Manoman auduga 65,000 za su amfana da rancen noma’
Rancen dai na damunar bana ne ta shekarar 2021.
Kungiyar Masu Saye da Sarrafa Auduga ta Kasa (COPMAN) ta kaddamar da bai wa manoman auduga kimanin 65,000 tallafi na rancen noma a Jihar Gombe.
Jami’in Babban Bankin Najeriya (CBN), Muhammad Nyako ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da rabon kayan noma a Gombe, inda yace wannan rance na damunar bana ne ta shekarar 2021.
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 40 a kauyukan Zamfara
- Mukabala: Yau za a yi ta ta kare tsakanin Sheik Abduljabbar da malaman Kano
A cewarsa, an zabi jihar Gombe ne don kaddamar da wannan shiri saboda ita kadai ce Jihar da take da kamfanonin gurzar auduga masu aiki har guda uku.
Jami’in ya hori manoman audugar da su tabbatar sun shuka irin kar ba wai su sayar ba domin bunkasa noman audugar ganin cewa iri ne aka basu mai inganci.
Daga nan sai ya roki jami’an tsaro da su taimaka wajen raka manoma da kayayyakin da aka basu zuwa gonakinsu, musamman ma takin saboda matsalar ababen hawa.
A nasa jawabin, Kwamishinan Aikin Gona na Jihar, Muhammad Magaji Gettado, ya ce babbar matsalar da ake fuskanta tsakaninsu da manoma ita ce ta rashin ba su cikakkun kayan da aka yi alkawari.
Magaji Gettado, ya kara da cewa sai an ilimantar da manoma kan iraruwa da magungunan shukar da za a basu domin a karfafa musu gwiwa ta yadda za su fahimci yadda ake amfani da su.
Ya ce gwamnatin Jihar tana bai wa harkar noman auduga muhimmanci kasancewar shi kan sa gwamnan manominta ne kuma mai safararta.
A nasa tsokaci shugaban Kungiyar COPMAN na kasa Alhaji Lawan Sani Matazu, cewa ya yi sun kaddamar da wannan shiri ne a Gombe saboda jihar Gombe ita ce kan gaba wajen noman auduga a kasar nan.
Matazu, yace noman Auduga hanyar ci gaba ne ga matasa domin yakan samar da aikin yi da kuma kudin shiga.