Manoman auduga dubu 100 za su ci gajiyar shirin ba da rance na Anchor Borrowers a bana

Gwamnatin Tarayya ta ce, shirin rancen noma na Anchor Borowers da Babban Bankin Najeriya (CBN) ke ba manoma, zai ba manoman auduga dubu 100 don noman auduga rancen kudin noman auduga a bana a duk fadin kasar nan. Minista a Ma’aikatar Masana`antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Hajiya A’isha Abubakar ce ta sanar da hakan a […]

Manoman auduga dubu 100 za su ci gajiyar shirin ba da rance na Anchor Borrowers a bana

Hajiya A’isha Abubakar, Minista a Ma’aikatar Masana`antu, Kasuwanci da Zuba Jari

Gwamnatin Tarayya ta ce, shirin rancen noma na Anchor Borowers da Babban Bankin Najeriya (CBN) ke ba manoma, zai ba manoman auduga dubu 100 don noman auduga rancen kudin noman auduga a bana a duk fadin kasar nan.

Minista a Ma’aikatar Masana`antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Hajiya A’isha Abubakar ce ta sanar da hakan a Zariya Jihar Kaduna  wajen wani taron yini daya na masu ruwa-da-tsaki kan in ganta noman auduga da  samar da iri mai nagarta a Najeriya kamar yadda Kamfanin Dillacin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito.

Taken taron shi ne “Inganta Hanyoyin Samar da Irin Auduga Mai Nagarta da Nufin Inganta Noman Auduga Don Bunkasa   Masaku a Nijeriya.”

Ministar wacce Daraktan Sashen Cinikayya da Samar da Kayayyaki (CPID) Misis Omololu Opeewe ta Ma’aikatar ta wakilce ta, ta ce, Gwamnatin Tarayya ta ba da fifiko kan yadda za a inganta noman auduga a kasar nan.

Ta ce, a kokarin Gwamnatin Tarayya na samar da hanyoyi daban daban na bunkasa tattalin arziki, ta fitar da wani tsari na bunkasa hanyoyin da za a bunkasa da kuma samar da sutura a kasar nan, da nufin bunkasa noman auduga da sarrafa shi a cikin kasar nan.

Ta ce, sashen kula da sabon tsari da shirin da gwamnati ta yi don bunkasa noman auduga ya gana da dukan hukumomi da ma’aikatu da sauran masu ruwa-da-tsaki da abin ya shafa, inda suka tsara irin shirye shirye da ayyukan da za a gudanar da nufin bunkasa masaku a Najeriya.

Ministar ta ce, yanzu haka ma’aikatar tana yin aiki da Kungiyar Manoman Auduga ta Najeriya (NACOTAN) da nufin samar da rancen noman auduga daga Bankin CBN a karkashin shirin bayar da rancen noma na Anchor Borowers, da nufin kara yawan audugar da ake nomawa ta hanyar kara samun kasuwa a harkar don samar da ayyukan yi da kuma tabbatar da cewa ana noma ta a kai a kai.

Hajiya A’isha Abubakar ta ce, karkashin shirin ana sa ran manoma dubu 100 kowannensu zai nomi akalla eka biyu na auduga a karkashin shirin ba da rancen a noman auduga na bana.

Ministar ta ce, a karkashin shirin ana sa ran za a rika noma tan daya da rabi na auduga a kowace eka ana kuma sa ran kamfanonin samar da iri za su samar da sama da tan dubu 300 na iri kuma za a samar da auduga tan dubu 114 ga masaku.

Ta ce, ana sa ran cibiyoyin binciken albarkatun noma na kasa (IARs) za su taka muhimmiyar rawa wajen samar da iri mai nagarta, yayin da cibiyar bincike da bunkasa harkokin noma ta kasa (NAERLS), ne za ta ba da horo ga manoman audugar domin samun nasarar shirin da aka sa a gaba.

Tun farko Daraktan Cibiyar Binciken Harkokin Noma (IAR) Farfesa Ibrahim Umar Abubakar ya ce, auduga na daga cikin kayayyakin noma na kasuwanci da bunkasa masana’antu,

Ya ce, bunkasa tattalin arzikin kasar nan ya dogara ne ga irin gudunmawar da aka samu ta fannin aikin gona, kuma ci gaban aikin gona ya dogara ne ga noman auduga.

Farfesa Ibrahim, ya ce a kasar nan akwai wurare da yawa da ake noman auduga kamar Legas da Kaduna da Kano, akwai kuma wasu birane da noman auduga ke yin tasiri kamar Funtuwa da Gusau da sauran garuruwa.

Noman auduga sana’a ce, mai matukar muhimmanci ga rayuwar ’yan Najeriya musamma manomin audugar ko mai sayar da irin auduga ko mai fataucin audugar da masu masaku da masana’antun yin sutura.

Farfesa Umar, ya ce noman auduga abu ne da ke taimakawa wajen biyan bukatun ’yan Adam saboda dan Adam yana bukatar abinci da matsugunni da sutura, kuma auduga tana daya daga cikin abin da ke biyan bukatar dan Adam ta fannin sutura kuma a gidaje ma auduga na biyan bukata. Saboda mafi yawa daga cikin wuraren da ake tsugunar da ’yan gudun hijira kamar su tamfol-tamfol da auduga ake yin su.

Daraktan ya ce, idan ana yi magana kan auduga mutane kan yi zaton zannuwa da yadduduka masu tsada ne da ake yin su a kasashen waje da sauransu amma a hakikanin gaskiya ana amfani da auduga ta hanyoyi da yawa kamar labule da mayafi da bargo da sauransu. Ya ce yau inda za a ce Najeriya za ta kware ta shahara wajen yin barguna kadai za ta shahara a tsakanin kasashen duniya.

Ya nuna damuwa kan yadda a yanzu ake shigowa da darduma da sshifidun daki iri iri daga kasashen Saudiyya, inda ya ce idan aka yi la’akari da dimbin kudaden da ake kashewa wajen shigo da wadannan kayayyakin a kowace shekara sai a ga kudade ne masu dimbin yawa in da suke taba kudaden musayar kasar nan.

Kamfanin dilancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa, mahalarta taron sun fito ne daga yankunan da ake noman auduga da sauran wurare.