Manoman auduga dubu 94 sun samu tallafi a Kano da Jigawa

Fiye da manoma dubu 94 da mafi yawancinsu matasa ne suka amfana da shirin Gwamnatin Tarayya na Anchor Borrowers a bangaren noman auduga a jihohin Kano da Jigawa. Wannan bayani yana kunshe ne a wata takarda dauke da sanya hannun mai magana da yawun wadanda suka ci gajiyar shirin, Yusuf Alhaji, inda ya ce sun […]

Manoman auduga dubu 94 sun samu tallafi a Kano da Jigawa

Auduga

Fiye da manoma dubu 94 da mafi yawancinsu matasa ne suka amfana da shirin Gwamnatin Tarayya na Anchor Borrowers a bangaren noman auduga a jihohin Kano da Jigawa.

Wannan bayani yana kunshe ne a wata takarda dauke da sanya hannun mai magana da yawun wadanda suka ci gajiyar shirin, Yusuf Alhaji, inda ya ce sun ci gajiyar ce  sakamakon kokarin Mataimakin Shugaban Kungiyar Manoman Auduga ta Najeriya (NACOTAN), Alhaji Munzali Dayyabu Taura, wanda ya kaddamar da bikin tantancewa na karfafa wa matasa shiga harkar noma.

Ya ce a cikin mutum dubu 151 a jihohi 28 na kasar nan da ke cikin shirin Anchor Borrowers, jihohin Kano da Jigawa kadai suna da mutum dubu 94 da suka ci gajiyar shirin saboda kwazo da jajircewar Alhaji Munzali Taura.

Wadanda suka ci gajiyar sun ce burin Mataimakin Shugaban Kungiyar ta Kasa ta shi ne ya shigar da matasa su rungumi harkar noman auduga, sannan a talalfa wa kamar mutum dubu 100 a jihohin Kano da Jigawa.

Matasan sun bayyana cewa burin manoma na noman auduga a karkashin shirin Anchor Borrowers kwalliya ta biya kudin sabulu a jihohin Kano da Jigawa musamman yadda matasa suka rungumi harkar saboda tsarin shugabancin Mataimakin Shugaban Kungiyar NACOTAN.

Wadanda suka ci gajiyar sun bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ci gaba da bai wa harkar noma kulawa saboda muhimmancinta ga al’ummar Arewa a bangaren tattalin arziki da yadda take samar  da ayyukan yi kai-tsaye.