Manoman citta sun bukaci tallafin gwamnati

  Shugaban Kungiyar Manoman Citta da Kasuwancinta (Ginger Growers and Marketers Association-GGMA), na Jihar Kaduna, Mista Solomon Jatau ya bukaci gwamnatoci a dukkan matakai su karfafa manoman citta ta hanyar tallafa musu don kara samar da cittar da za ta yi daidai da bukatar cikin gida da na kasuwannin duniya. Shugaban ya yi wannan kira […]

Manoman citta sun bukaci tallafin gwamnati

 

Shugaban Kungiyar Manoman Citta da Kasuwancinta (Ginger Growers and Marketers Association-GGMA), na Jihar Kaduna, Mista Solomon Jatau ya bukaci gwamnatoci a dukkan matakai su karfafa manoman citta ta hanyar tallafa musu don kara samar da cittar da za ta yi daidai da bukatar cikin gida da na kasuwannin duniya.

Shugaban ya yi wannan kira ne a wata takarda da aka raba wa manema labarai a garin Kafanchan, inda ya ce cittar da ake nomawa a Najeriya tana daga cikin mafiya kyau a duniya ta yadda take da karbuwa a kasashe daban-daban, inda ya ce idan aka tallafa wa manomanta hakan zai yi matukar amfani wajen bunkasa tattalin arzikin kasar nan.

Ya ce, bisa la’akari da kokarin da wannan gwamnati ke yi wajen kyautata rayuwar talaka ta hanyar bunkasa harkar noma, idan aka tallafa wa kungiyar ta kasa a karkashin jagorancin Dokta Florence Edwards, wadda take kokari wajen amfani da dukiyarta don tallafa wa manoman, zai rage yawan dogaro da gwamnati da jama’a musamman manoma ke yi.