Manoman dankali sun yi zanga-zangar kan faduwar farashi a Bangaladesh
Manoman dankali sun yi zanga-zangar nuna takaicin faduwar farashi a Bangaladesh, inda suka soki gwamnati kan kin tabbatar musu da tsayayyen farashin mai kyau na kayansu Sannan sun bukaci gwamnati ta rika sayen dankali daga garesu, don rage wa manoman karsashin asarar da ta kai ta kimanin kilo miliyan daya da rabi, daga cikin kilo […]

Manoman dankali sun yi zanga-zangar nuna takaicin faduwar farashi a Bangaladesh, inda suka soki gwamnati kan kin tabbatar musu da tsayayyen farashin mai kyau na kayansu Sannan sun bukaci gwamnati ta rika sayen dankali daga garesu, don rage wa manoman karsashin asarar da ta kai ta kimanin kilo miliyan daya da rabi, daga cikin kilo miliyan shida da suke samarwa, kamar yadda jaridar Dailystar ta ruwaito.
kungiyar Manoman Bangladesh ta Krishak Samity, ita ta shirya wannan zanga-zangar a cibiyar ’yan jarida ta kasa (National Press Club).
“A ware kudi daga asusun musamman da ke karkashin kulawar Firayiminista, don kafa cibiyoyi a yankunan karkara, wadanda za su rika sayen dabnkali daga hannun manoma,” a cewar shugaban kungiyar manoman Bangladesh, Morshed Ali.
Mafi yawan manoman ba za su iya alkinta dankalinsu na tsawon lokaci ba, don haka dole su sayar don biyan basusssukansu, wadanda suka karba don aikin gona, a cewarsa.
A Nuwamba da Disambar bara, manoma da dama sun dakatar da nomansu saboda matsalolin da suke fuskanta. Masu na’urorin alkinta kayan abinci ba za su iya adana musu kayan amfaninsu ba, saboda rikicin siyasa da kasar ta samu kanta a ciki, daidai lokacin da aka gudanar da zaben kasa. Da wutar rikicin siyasa ta lafa, sai manoma suka ci gaba da noman dankali, su ma masu alkinta kayan, suka fara fitar da tsohuwar ajiya da firjinsu. Yawan kayan amfani da aka baza a kasuwanni shi ya haifar da karewar farashin dankali a kasr Bangladesh.
Sai dai har yanzu masu fitar da dankalin zuwa kasashen ketare, karyewar farashin bai same su ba.