Manoman dawa a Kano na murna da sabon irin Cibiyar Bincike ta IAR

Manoman dawa na cike da murna bayan da Cibiyar Binciken Aikin Gona ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta samar da wani sabon irin dawa, wanda ake iya nomawa kuma a girbe a cikin ƙasa da wata uku. Sabon irin ya hada da SAMSORG 52, SAMSORG 53 da kuma SAMSOORG 54 a wani ƙoƙarin […]

Manoman dawa a Kano na murna da sabon irin Cibiyar Bincike ta IAR

Manoman dawa na cike da murna bayan da Cibiyar Binciken Aikin Gona ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta samar da wani sabon irin dawa, wanda ake iya nomawa kuma a girbe a cikin ƙasa da wata uku.

Sabon irin ya hada da SAMSORG 52, SAMSORG 53 da kuma SAMSOORG 54 a wani ƙoƙarin cibiyar na samar da irin dawa mai gajeren zango da za a iya girebewa tare da gero da sauran kayan amfani gona domin inganta aikin gona da yaƙi da dumamar yanayi.

Manoman da ke Bagadawa da ke Ƙaramar Hukumar Dawakin

Tofa sun nuna farin cikinsu da samar da sabon irin dawar ’yar wuri lokacin da cibiyar binciken ta yi musu wani gwaji a yankin.

Wani Manomi, Alhaji Danliti Dawanau ya ce, sabon irin da aka shuka a gonarsa ya ba shi mamaki domin bayan kwani 32 da shuka tsohon irin dawar, sabon irin da aka

shuka ya nuna cewa sai an fara girbe sabon irin kafin irin daminar badi”.

Da yake jawabi wajen ƙaddamar da irin, Darektan Cibiyar ta IAR, Farfesa Ado yusuf ya ce gwajin ya taimaka wajen wayar da kan manoma kan sabon irin da kuma yadda zai haɓaka aikin gona.

Darekatan, wanda mataimakinsa, Farfesa Lucious Joseph Bamaiy ya wakiltai ya ce, an samar da sabon irin samfurin SAMSORG 53, wanda shukarsa ke nuna a cikin kwana 95 zuwa 100 a 2023. Kazalika ana iya noma irin a yankunan Gabashi da Arewacin Afirika.

A nasa jawabin, Shugaban Cibiyar Binciken Kayan Amfanin Gona ICRISAT, Dakta Angarawai Ignatius cewa ya yi, dalilin samar da sabon irin shi ne domin manoma su fuskanci ƙalubalen dumamar yanayi da na tsaro a sassan ƙasar nan, inda aka yi la’akari da saurin girman shuka daga irin dawar a yanayi na rashin ruwa.

Ya ce, cibiyar ta karɓi tayin da ƙalubalen da dumamar yanayi suka bujiro da su wajen yin nazari da bincike a kan sabon irin dawar da za a iya shukawa da wuri kuma a girbe da wuri domin kare gonaki daga zama maɓuyar miyagu da ɓata-gari.

Daga Ibrahim Musa Giginyu da Ahmad Datti, Kano Fassara: Ahmed Ali, Kafanchan