Manoman gero a Jihar Sakkwato sun dara a bana
Yanzu da aka kammala girbin gero a Jihar Sakkwato, kuma kakarsa ta kankama manoman gero sun dara a bana. Sai dai sun yi kira ga manoma ’yan uwansu su guji sayar da geron ga ’yan baranda masu sayen geron da yawa, ba don bukatun yau da kullum ba, sai don su boye in ya yi […]
Yanzu da aka kammala girbin gero a Jihar Sakkwato, kuma kakarsa ta kankama manoman gero sun dara a bana. Sai dai sun yi kira ga manoma ’yan uwansu su guji sayar da geron ga ’yan baranda masu sayen geron da yawa, ba don bukatun yau da kullum ba, sai don su boye in ya yi tsada a gaba bayan kakar ta wuce su fitar suna sayar wa jama’a da muguwar tsada.
A ziyarar da wakilinmu ya kai wasu wurare ya tabbatar da cewa an samu gero mai yawa da ake iya sa ran samun wadataccen gero a jihar.
Alhaji Maidamma Aliyu Hakimin Kauran Miyo a Karamar Hukumar Bodinga sanannen manomi ne a yankin, ya ce “A wannan lokacin da gero ya nuna, wadansu manoma sun girbe geronsu sun yanke sun adana, yayin da wadansu ke kan yin aikin ba su gama ba. Mutane sun yi farinciki da wannan daminar don ta zo ne a lokacin da ake bukatar abinci a kasar nan. An samu ruwan sama sosai da wuya a samu kwana uku a jere ba a yi ruwa mai karfi ba, abin da ya sanya muka ji karfi a jikinmu mun gode Allah da Ya ba mu amfanin gona a wannan shekarar fiye da bara.”
A kauyen Manoma da ke Karamar Hukumar Wurno, Malam Ahmadu ya tabbatar da cewa mutanen yankinsu sun samu gero sosai a bana.
“Mafi yawan manomanmu sun yi farinciki da abin da suka samu na amfanin gero a bana, an samu ruwan sama sosai da ya taimaka ga wannan nasara. Yanzu muna shirin gibar dawa dadibar wake wannan zafin da ake yi su ne ake yiwa don suna bukatarsa,” inji shi.
Malam Bello Abubakar mai shekara 58 manomi ne da yake noma gonakinsa hudu a Karamar Hukumar Dange-Shuni, ya ce a bana ya samu amfanin gero fiye da bara. Ya ce ya samu buhu fiye da 150 sabanin baya da bai wuce buhu 45, yana ganin nasarar ta samu ne sakamakon ruwan sama da aka samu da canja irin gero da suka yi.
Malam Tukur Umaru da ke Gwamfa Dangara ya ce, su abin ya sha bamban, domin manoma a kauyensu ba su yi shuka da wuri ba, don tsoron kada karancin ruwan da aka samu a bara a samu a bana.
Tukur wanda ya ce ya kwashe shekara 30 yana noma ya ce amma a wasu kauyuka abin sai sam barka “Irin su Gidan Yaro da Mallamawa da Gidan Yamma da Gidan Doki duk sun samu amfani kuma ga ruwa ba a san abin da ma za a yi da shi ba, kan haka muke son su mayar da hasararmu ga noman ranin da za mu shuka shinkafam da albasa da tonka da fatan samun nasara,” in ji shi.
Shugaban Kungiyar Manoma ta Jihar Sakkwato Alhaji Murtala Gagadu Minanata ya bayyana wannan damina a matsayin gamsasshiya da aka samu gero mai yawa.
“Manoma a Sakkwato sun yi sa’a sun samu amfani ba kamar bara ba, a wasu wuraren. An samu ruwan sama ba yankewa da ya ninka na bara kusan uku ga yabanya mai kyau, a ko’ina a Jihar Sakkwato kamar yadda muka samu labari daga shugabaninmu na kananan hukumomi.
Alhaji Murtala ya kara da cewa, “Bayan ruwan sama da aka samu Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya samar da taki ga manoma a lokacin da ya dace, abin da ya kara taimakawa ga samun amfani mai yawa. Kwanon geron da ake sayarwa Naira 350 zuwa 400 yanzu ya koma 200 wani wurin 220 har 180 kana samu a wasu kauyuka,” inji shi.
Shugaban manoman ya gargadi manoma a kan su guji sayar wa ’yan baranda geron wadanda za su boye shi.
Kuma ya shawarci Musulmi su tabbatar sun fitar da Zakka ga wanda ya samu abin da ya kai nisabi. “Manoma za su iya fitar da zakkarsu ta hanyar kwamitin zakka na gunduma domin taimaka wa marasa karfi da yakar talauci a jiha. Muna yi wa Allah godiya kan wannan albarka da Ya ba mu a bana, muna sa ran samu haka a dawa da sauran abincin da ba mu girbe ko cire ba,” inji Gagadu.