Manoman Kaduna sun yi alkawarin samar da tan dubu 15 na auduga a bana

Kungiyar Manoman Auduga ta Kasa (NCAN) Reshen Jihar Kaduna, ta yi alkawarin samar da tan dubu 15 na auduga a bana.                                                                                                                                               Shugaban riko na kungiyar, Alhaji Auwalu Wappah ne ya sanar da haka yayin tattaunawarsa da manema labarai kan shirin noman auduga da ke ci gaba da gudanarwa a Zariya da fadin jihar. Ya ce, […]

Manoman Kaduna sun yi alkawarin samar da tan dubu 15 na auduga a bana

Auduga

Kungiyar Manoman Auduga ta Kasa (NCAN) Reshen Jihar Kaduna, ta yi alkawarin samar da tan dubu 15 na auduga a bana.                                                                                                                                               Shugaban riko na kungiyar, Alhaji Auwalu Wappah ne ya sanar da haka yayin tattaunawarsa da manema labarai kan shirin noman auduga da ke ci gaba da gudanarwa a Zariya da fadin jihar.

Ya ce, samar da wannan adadi na auduga abu ne mai yiwuwa idan aka yi la’akari da kwarin gwiwa da tallafin da kungiyar ke samu daga gwamnati, inda ya ce tuni manoman suka shirya tare da shan alwashin tabbatuwar haka.

“Muna da akalla mambobi dubu 15 da suka yi rajista da mu wadanda akalla manoma dubyu 10 daga ciki za su bai wa shirin muhimmanci. Shirin bayar da bayanai kan asara da kuma rancen aikin gona (NIRSAL) da Babban Bankin Najeriya CBN, ne za su samar da dukan abubuwan da manoman ke bukata tare da tallafin kudaden gudanar da aikin,” inji shi.

Ya bayyana cewa daga cikin kananan hukumomi 23 na jihar ta Kaduna, 17 na noman auduga sannan 15 daga ciki suna cikin wannan shirin, in ban da kananan hukumomin Kachiya da Zangon Kataf wandanda har yanzu ba su shigo cikin shirin ba.

Ya shawarci manoman auduga da ke a fadin jihar su yi amfani da wannan damar su shigo cikin shirin don amfanar kansu da Jihar Kaduna da kuma kasa baki daya kafin kammala shirin.