Manoman karkara a Taraba sun koka da rashin hanyoyi
Manoma karkara a Jihar Taraba sun koka kan rashin hanyoyin mota, matsalar da suka ce tana kawo masu cikas wajen fidda amfanin gonakinsu zuwa kasuwa, binciken da wakilin Aminiya ya gudanar a kananan hukumoin Ardo Kola da Gassol da Bali da Ibbi da Karim Lamido. Manoman da wakilinmu ya zanta dasu sun bayyana cewa rashin […]
Manoma karkara a Jihar Taraba sun koka kan rashin hanyoyin mota, matsalar da suka ce tana kawo masu cikas wajen fidda amfanin gonakinsu zuwa kasuwa, binciken da wakilin Aminiya ya gudanar a kananan hukumoin Ardo Kola da Gassol da Bali da Ibbi da Karim Lamido.
Manoman da wakilinmu ya zanta dasu sun bayyana cewa rashin hanyoyin mota a yankunan su na haifar masu da matsalolin masu yawan gaske.
A cewar wani manomi da ke garin Makurna a Karamar hukumar Gassol, mai suna Mustapha Garba masu motoci haya da babura suna karban kudade masu yawa a wajen manoma in an dauki hayarsu don fita da kayan gona zuwa kasuwanni.
Ya kara da cewa, a hanyar da ke da kwalta ana karban naira dari biyu akan buhu daya a tafiya mai nisan kilomita goma, amma da yake hanyarsu ba kwalta naira dari biyar suke biya daga Makurna zuwa garin Mutum-Biyu saboda rashin kyan hanya.
Wani manomi da ke bayan kogin Benuwe a Karamar hukumar Karim Lamido, mai suna Alhaji Garba Sarkin noma shi ma ya koka kan irin wahalar da manoma a yankin karamar hukumar suke fuskanta a sanadiyyar rashin hayar mota.
Ya ce, sukan dauko amfani gonarsu akan babura daga gidajensu su kawo bakin kogi sannan su sa kayan a cikin jirgin ruwa.
Alhaji Garba Sarkin noma ya bayyana cewa, daga nan kuma Sai a sake daukan kayan a babura zuwa Kasuwa wanda yasa suke shan wahala tare da yin asaran kayan gona akan hanya zuwa kasuwanni.
Ya bukaci gwamnatin Jihar Taraba ta maida hankali wajen samar da hanyoyin mota a yankunan karkara don bunkasa tattalin arzukin mazauna kauyuka tare da inganta rayuwar al’ummar karkara.
Da yake mai da martani kan koke-koken manoma mazauna yankunan karkara, mai bai wa gwamnan Jihar shawara kan watsa labarai, Mista Bala Dan Abu, ya ce gwamna Darius Ishaku yana iyaka kokarinsa wajen samar da abubuwan more rayuwa ga al’ummar da suke zaune a yankunan karkara.
Ya ce samar da hanyoyin mota da kayan aikin gona na daga cikin ayyukan da gwamnatin jihar a karkashin jagorancin Gwamna Darius Ishaku ta sa a gaba.