Manoman Kifi a Jihar Sakkwato na fuskantar matsaloli
Manoman kifi a Jihar Sakkwato na fuskantar dimbin matsalolin rashin wurin kiwo da kayan amfani na kiwon da zai sa mutum ya amfana da harkar. Kungiyar Masunta ta Jihar Sakkwato ce ta bayyana haka inda ta koka kan matsalolin tana bukatar a magance musu su. Mai magana da yawun kungiyar Alhaji Kabiru Muhammad ya ce […]
Manoman kifi a Jihar Sakkwato na fuskantar dimbin matsalolin rashin wurin kiwo da kayan amfani na kiwon da zai sa mutum ya amfana da harkar.
Kungiyar Masunta ta Jihar Sakkwato ce ta bayyana haka inda ta koka kan matsalolin tana bukatar a magance musu su.
Mai magana da yawun kungiyar Alhaji Kabiru Muhammad ya ce “Babban kalubalen da ke cikin harkar ba a bunkasa ta, ba a samar mana da sababbin iri daban da wadanda muka sani. Masuntanmu na gida da ke garin Kware da Kwalkwalawa kullum irin kifi guda ne suke kamowa, muna so a bunkasa sana’ar tamu da wasu nau’o’in irin kifaye da kuma kayan kamun kifin”.
Kakakin kungiyar ya ce a lokacin gwamnatin Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko sun samu abin kamun kifin guda 20. Ya ce abin bai wadace su ba a kungiyar da take bukatar guda 85.
Ya bayyana yunkurin da suke yi a yanzu ko za su samu kayan “A zaman tattaunawa da muka yi da jami’an Ma’aikatar Kula da Kiwon Kifi sun yi mana alkawarin bunkasa kiwon kifin. Mun mika kokon bararmu gare su na samar da kayan kiwon kifin ga mambobinmu wadanda mafi yawansu tsofaffin ma’aikata ne da ke da sha’awar shiga harkar kiwon kifi,” inji shi.
Muhammad ya ce samar da kayan kiwon kifi ne kadai zai bunkasa harkar har a samu gudunmawa a bangaren don samar da abinci wadatacce a Jihar Sakkwato.
“Saboda muhimmancin kifi ga al’umma bai kamata a yi masa rikon sakainar kashi ba, yana cikin manyan abinci masu gina jiki, yana inganta rayuwar mutanenmu,” inji shi.
Mustafa Muhammad mai shekara 40 wanda ya ce ya tashi cikin kamun kifi, masunci ne a Gulbin Kainuwa da ke Karamar Hukumar Kware a Jihar Sakkwato, inda ya koka kan kalubalen da suke fuskanta a bangarensu na Kware daga wurin da gwamnatin jihar don bunkasa kiwon kifi.
Ya ce “Akwai bukatar kawar da Shalla (dogon haki) da ke wurin gaba daya da dambar da ta yi yawa tana hana kamun kifi a gulbin.”
Ya ce yana sane wata shida da suka gabata gwamnatin jihar ta fito da shirin bunkasa noman kifi a bangaren Kware kuma ta fahimci abin da ya zama karfen kafa a noman kifin.
“Gaskiya ce jami’an Ma’aikatar Kula da Lafiyar Dabbobi da Kiwon Kifi, sun zo sun zuba irin kifi a Gulbin Kainuwa, wadansu ma daga karamar hukuma sun zuba iri daban-daban a cikin ruwan, su yi magana da Sarkin Ruwanmu kada a yi kamun kifi tsawon wata shida haka muka aminta ba wanda ya yi su a tsakanin lokacin da suka bayar,” inji shi.
Ya ce bayan lokacin da suka bayar ya cika suka dawo da zimmar za su kwashi garabasa. “Amma da muka zo kamun kifin mun fahimci igiyar ruwan da ta gitta a ruwan ta sanya kamun kifi na yi mana wahala, a karshe dai ba mu amfana ba,” inji shi.
Shugaban masu sayar da kifi Alhaji Badamasi Bello Kofar Kware ya roki gwamnatin jihar ta ba su tallafi a harkar noman kifi.
“A lokacin da gwamnati ta bai wa manoma tallafin kayan noma ya kamata ta hada da masu kiwon kifi. noman kifi sana’a ce a jihar nan da ke taimaka mana,” inji shi.
Kwamishinan Ma’aikatar Kula da Lafiyar Dabbobi da Kiwon Kifi, Farfesa Abdulkadir Junaid ya sanar da kudiri da shirye-shiryen gwamnati kan bunkasa kiwon kifi, inda ya bayyana kiwon kifi a matsayin daya daga cikin abubuwan da tsawon lokaci aka fita batunsa. Ya ce kan haka ma’aikatarsa ta ware wasu wurare a kananan hukumomin Wamakko, da Binji da Kware da sauransu inda za ta yi aiki kansu domin dawo da kiwon kifi gadan-gadan.
Kwamishinan ya fitar da manufarsa ta hadin gwiwa da kungiyar da sauran masu ruwa-da- tsaki don bunkasa fannin.