Manoman masara dubu 10 sun ci gajiyar noma don kasuwanci a Jihar Kaduna
Babban jami’in shirin noma don kasuwanci a Jihar Kaduna Alhaji Lawal Umaru Abdulsalam ya ce zuwa yanzu sama da manoman masara dubu 10 ne suka ci gajiyar shirin nan na noma don kasuwanci a jihar.Alhaji Lawal Umaru Abdulsalam ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga manoman da suka ci gajiyar shirin a […]
Babban jami’in shirin noma don kasuwanci a Jihar Kaduna Alhaji Lawal Umaru Abdulsalam ya ce zuwa yanzu sama da manoman masara dubu 10 ne suka ci gajiyar shirin nan na noma don kasuwanci a jihar.
Alhaji Lawal Umaru Abdulsalam ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga manoman da suka ci gajiyar shirin a garin Saminaka, inda ya ce wannan shiri na noma don kasuwanci da suka bai wa manoma iri ingantatce da takin zamani da maganin ciyawa da shanun huda ya samu gagarumar nasara a Jihar Kaduna. Kuma ya ce manoman da suka ci gajiyar sun samu karin amfanin gonar da suke nomawa.
Alhaji Lawal Umaru ya yi bayanin cewa a yanzu an kara wa shirin na noma don kasuwanci shekara biyu. “Kuma a yanzu za mu zabi manoma ne da suke noma da gaske don cin gajiyar wannan shiri. Don haka tallafin da za mu bayar zai danganata ne ga kwazon manomi da kuma ajiye bayanai kan abubuwan da yake yi tun daga sharar gona har zuwa lokacin da ya sayar da masarar da ya noma,” inji shi.
Ya ce ganin a Jihar Kaduna babu inda ake noman masara kamar yankin Saminaka a wannan sabon shirin noma don kasuwanci za su gina wani katafaren wurin tara masara a yankin. Domin idan masu sayen masara sun zo su samu wajen da za su rika zuwa suna
sayen masarar maimakon su rika zuwa kasuwanni suna saya.
Babban jami’in ya yi bayanin cewa sun je yankin ne, don su ga manoman da suka ba su tallafi a bangaren noman masara, domin ganin abubuwan da suka yi da abubuwan
da suka samu kan kafin tallafin da aka ba su.
Ya yi kira ga manoman cewa su sani sana’ar noma babbar sana’a ce da ya kamata su rike hannun bibbiyu.