Manoman masara sun samu horon kwanaki biyu a Abuja
Kungiyar manoman masara ta kasa wato “Maize Association of Nigeria” (MAAN) ta shiryawa mambobinta horo na kwanaki biyu a Abuja, inda masana a harkar su ka gabatar da lakcoci da makkloli akan yadda za su bunkasa amfaninsu don cike gibin adadin masara da kasar nan ke bukata da kuma magance shigo da ta waje. Da […]

Kungiyar manoman masara ta kasa wato “Maize Association of Nigeria” (MAAN) ta shiryawa mambobinta horo na kwanaki biyu a Abuja, inda masana a harkar su ka gabatar da lakcoci da makkloli akan yadda za su bunkasa amfaninsu don cike gibin adadin masara da kasar nan ke bukata da kuma magance shigo da ta waje.
Da ya ke jawabi a yayin bude taron, wanda ya gudana a ranakun Talata da Laraba, shugaban kungiyar mai barin gado, Fasto Tunje Adenola ya ce muhimmin abu da manoman kasar nan ke bukata don gogayya da takororinsu na ketare shi ne wadata su da kayayyakin noma a farashi mai sauki sannan wanda zai habaka masu girbi.
“Idan haka ta samu ina tabbatarwa gwamnati cewa ba wani kamfani da zai gwammace shigo da amfanin gona daga waje a maimakon ya sayi na gida, saboda yin hakan zai kai shi ga asara a maimakon samun rangwame. daya daga cikin masana da su ka gabatar da jawabai a yayin taron, Farfesa Dele Fakorede daga Jami’ar Obafemi Awolowo da ke Ile-fe ya yi suka akan yadda gwamnati da kuma wasu kungiyoyin noma na duniya ke dogaro da bayanai da ya bayyana a matsayin na baya, don aiwatar da kasafinsu a tsarin noma, inda ya bukaci da su rika kaiwa ga cibiyoyin bincike a fagen, maimakon dogaro kacokam akan wadancan.
Dokta Wale Awotide wanda mamba ne a kwamitin masana na kungiyar, ya gargadi manoma da su guji share wajen noma da ya fi karfin aljihunsu, inda ya bada misali kamar haka: “Idan ka san hekta guda a gonarka na bukatar buhun taki kamar 8, sannan karfin aljihunka bai wuce na buhu 4 ba, abinda ya kamata ka yi shi ne ka yi noma a rabin wajen, saboda shi ne zai baka tabbacin riba a maimakon noma wajen gabadaya da ka iya zame maka asara, inji masanin.
Shugaban kungiyar MAAN na Jihar Katsina, Alhaji Bello Abubakar wanda ya yi bayani akan nasarar da kungiyarsu ta samu a sakamakon tafiya a dunkule, ya bayyana cewa mambobinsu wadanda adadinsu ya kai dubu 10 da 500, sun samu nasarar noma fili mai girman hekta dubu 22, inda wani kamfani mai suna WAPCO ke samar masu da kayayyakin aikin noma irinsu taki da iri da kuma magungunan feshi, sannan kuma ya saye amfanin gonar bayan sun yi girbi akan farashi da su ka yi matsaya akai.
Sauran wadanda su ka gabatar da jawabai a yayin taron sun hada da shugabannin kungiyoyin masu kiwon kaji na kasa, Mista Ezekiel Ibrahim da na Waken Soya, Mista Ayodele Uwala da wani masani akan noman masara, Dokta Sam Ojala da kuma shugaban wani kamfani mai harkan sayan kayan abinci, Cif Emmanuel Ijewere. Taron kungiyar a ranar Laraba wanda na sirri ne, ya fi maida hankali ne akan zaban sabbin shugabannin kungiyar ta kasa, inda aka tsara baiwa yankin Arewa maso Yamma kujeran shugabancin kungiyar.