Manoman Najeriya za su iya wadata kasa da tumatir – Sani Dangote
Shugaban Kungiyar Masu Hada-hadar Kayan Amfanin Gona ta Kasa (NABG) Alhaji Sani Dangote ya ce, manoman Najeriya za su iya samar wa kasar nan tumatir din da ake bukata ba tare da an shigo da shi daga kasashen waje ba. Alhaji Sani Dangote ya bayyana haka ne a wajen taron masu ruwa-da-tsaki kan noman tumatir […]
Shugaban Kungiyar Masu Hada-hadar Kayan Amfanin Gona ta Kasa (NABG) Alhaji Sani Dangote ya ce, manoman Najeriya za su iya samar wa kasar nan tumatir din da ake bukata ba tare da an shigo da shi daga kasashen waje ba.
Alhaji Sani Dangote ya bayyana haka ne a wajen taron masu ruwa-da-tsaki kan noman tumatir da aka gudanar a Kano a karshen makon jiya. Taron an shirya shi ne da nufin lalubo hanyoyin da za a bi don shawo kan matsalolin da suke kawo wa noman tumatir cikas.
Sani Dangote wanda shi ne mai babban kamfanin sarrafa tumatir na Dangote da ke Kadawa a Jihar Kano ya ce kasar nan tana da duk abin da ake bukata wajen noman tumatir wanda har ma za a iya fitar da shi waje.
A cewar Dangote, rashin fara aiwatar da dokar nan ta hana shigo da kaya daga kasar waje da Shugaban Kasa ya yi shekara biyu da ta gabata na daga cikin abin da ya janyo wa harkar noman tumatir matsala. “Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sa hannu a kan dokar amma saboda bangarori na aikin gwamnati sun hana a yi aiki da ita wanda hakan ba karamar matsala ba ce. Muna sanar da gwamnati cewa har yanzu masu shigo da tumatir daga kasar China suna ci gaba da kawowa ta barauniyar hanya. Su suka san hanyoyin da suke bi wajen shigo da kayansu kuma suna cin karensu ba babbaka. Bayan makudan kudaden da suke samu amma ba su iya biyan kasa haraji. Muna fata gwamnati za ta dubi wannan domin hakan zai bunkasa noman tumatir a fadin kasar nan,” inji shi.
Dangote ya kara da cewa, “A yanzu kamfanina na tumatir yana ci gaba da gudanar da aiki da tumatir din da muke samu a gida. Mun kuma fito da hanyar da za a bunkasa noman tumatir ta hanyar kawo iri da rainonsa inda muke raba wa manoman tumatir.”
“A kwanakin baya mun fuskanci matsalar rashin kamawar irin amma a yanzu idan aka shuka iri 100 ana samun 95 suna kamawa. A yanzu manoma sun rungumi noman domin ganin alfanunsa. A da idan manomi ya shuka kadada daya yakan samun kamar tan 10 a yanzu kuwa yana iya samun tan 50 zuwa 60 ka ga ko farashi ya sauka zai samu riba saboda ya samu karuwar yawan kaya,” inji shi.
Ya ce, “Idan tumatir ya fara fitowa akwai farashin da muke saye daga hannun manoma wanda farashin a kullum hawa yake. Misali idan ya fara da Naira 100 gobe zai zama 200. To yayin da ya kai misali Naira 300 ba mu iya saye saboda ya wuce farashin da za mu iya saya mu sarrafa. Sai su rika kai shi Legas don sayarwa a kasuwa. Kasancewar ita kuma masana’anta tana son ci gaba da aiki sai ya zama ba ta da zabi sai dai ta saya a hannun wadanda suka shigo da shi daga kasashen waje wanda kuma a wannan lokacin na san yakan fi na gidan arha. A wannan lokaci kuma su kuma manomanmu na gida sai nasu kayan ya karye kasancewar ga yawan tumatir din ga shi kuma babu ciniki.
Amma idan gwamnati ta hana shigo da tumatir daga waje hakan zai taimaka wa manoma kasancewar ko nawa farashin kayansu ya kai dole ne a saya domin babu wanda zai kawo daga waje ballantana ya karyar da nasa.”
A jawabin Shugaban Kungiyar Manoman Tumatir ta Kasa (TOGAN) Alhaji Abdul Ringim ya ce idan har ana so a shawo kan matsalar farashin tumatir, to sai an samar da wani teburin tattaunawa a tsakanin manoman da masu masana’antun sarrafa tumatir. “Tun kafin a yi shuka ya kamata a zauna a tsakanin manoma da masu sarrafa tumatir a kan yadda farashin tumatir din zai kasance.
Wannan kuma zai iya yiyuwa a rage ko a kara, tunda shi aikin noma gaba dayansa aiki ne na da za a dogara da abin da Ubangiji zai yi,” inji shi. Shugaban ya kara da cewa “Abin da manoma ke so shi ne tallafi musamman na bashi wanda manomi zai samu ba tare da an tursasa shi ya bayar da wata jingina wanda kuma ba shi da ita ba.”
A jawabin Ministan Ayyukan Gona Cif Audu Ogbeh ya ce, gwamnati tana yin kokari wajen magance wa manoma matsalar iri, inda ta dauki matakin tallafa wa Sashen Ayyukan Noma na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. “Sanin cewa babu abin da manomi yake bukata kamar iri ya sa gwamnati take kokarin tallafa wa Sashen Ayyukan Gona na ABU don ya bunkasa samar da iri. Haka kuma gwamnati za ta tabbatar cewa duk takin da ya zo kasar nan daga kasashen waje mai kyau ne ba za a kawo gurbatacce ba,” inji shi. A cewar Ministan Gwamnatin Tarayya za ta kara tallafa wa Bankin Manoma don bunkasa ayyukan noma a kasar nan.