Manoman rani a Sakkwato sun nemi taimakon gwamnati

kungiyoyin sa kai kan harkokin noma da abinci na tarayar Najeriya sun yi hasashen jihohi 16 har da Sakkwato za su fuskanci karancin abinci a shekarar 2018. Kan wannan hasashen na masanan ne Aminiya ta zanta da wasu dadaddun manoman rani kuma hakiman fadama a Jihar Sakkwato. Muhammad Lawali manomi ne da ya fi bayar […]

Manoman rani a Sakkwato sun nemi taimakon gwamnati

kungiyoyin sa kai kan harkokin noma da abinci na tarayar Najeriya sun yi hasashen jihohi 16 har da Sakkwato za su fuskanci karancin abinci a shekarar 2018. Kan wannan hasashen na masanan ne Aminiya ta zanta da wasu dadaddun manoman rani kuma hakiman fadama a Jihar Sakkwato.

Muhammad Lawali manomi ne da ya fi bayar da karfi ga noman shinkafa da alkama da kankana tun tashinsa a cikin noma yake, yakan noma buhu 100 har 150 amma a wannan shekarar da kyar zai iya samun buhu daya shinkafar ta bushe don ba ruwa, koramarsu ta samu matsala gulbi ya canja hanya hade da na Rima.

“Mun yi ta korafi ga gwamnati kan matsalar koramarmu mun samu shugaban farfado da aikin gona a Jihar Sakkwato, Alhaji Ciso Dattijo mun fada masa daga nan kofar Kware da Kabobi da Girebshi da Wamakko suna kan gulbin koramar ta shafe su, cikin gulaben dake biyowa anan guda biyar daya ne kawai, yanzu shi ma nan da lokaci kadan zai dauke nan ya koma na Rima, in hakan ta faru abu ne mai muni a jiha don ana iya samun karancin abinci, mu zamu rasa ruwa a fadamominmu kayanmu zasu bushe can kuma kayan nomansu zasu lalace, ruwa sun yi yawa hasara biyu kenan. Ya ce mana ya san da lamarin magana tana hannun gwamna zai yi kokari, amma har yanzu ba a yi komai ba ga abin da muke tsoro ya fara tabbata, shinkafarmu ta bushe sosai” a cewarsa.

Ya ci gaba da cewa yana cikin kungiyar manoma ta jihar Sakkwato hasalima shi shugaba ne a wata kungiya da ya ci gajiyar irin shinkafa da taki da irin alkama da aka ba shi wanda ba mai kyau ba ne an ce za a ba shi kudi har yanzu shiru. “Maganar fuskantar karancin abinci ba shakku kan maganar ilmi, kuma wannan rashin ruwan baiwa shinkafa a wurinmu, yana iya hadasa karancin matukar gwamnati ba ta yi wani abu ba na gyara gulbin nan shekara biyu sai dai labari gulbin ya kwafe,” in ji Hakimin Fadama Sarkin Taru.

Sambo Yahaya Aliyu manomin shinkafa da alkama da albasa ne tsawon lokaci tun tashinsa a gidansu noman da ya samu kenan yana cikin kungiyar manoma da suka taba samun tallafin gwamnati. 

“An tallafawa kungiyarmu taki da iri da kudi duk da wasu na korafin ba su samu ba don an fi baiwa manoman da ba na gaskiya ba. Kan hasashen masana gaskiya ne ana cikin karancin abinci a yankinmu saboda gulbinmu ya yanke ya yi wata korama, abincinmu ya bushe muna kira ga gwamnati ta taimaka kar mu shiga wani hali an fara samun karancin abinci sanadin rashin ruwan” a cewarsa. 

Haka kuma Alhaji Muntari Abubakar Kofar Kware, manomin albasa, wake, dankali da shinkafa ya ce “In har mun shiga cikin jerin jihohin da za su fuskanci karancin abinci to da wuya ba don wannan gulbin ya yanke ba ne kuma hasashen na iya tabbata, ganin wannan shekarar ba a yi noma sosai ba a bangarenmu mafiyawan wadanda suka yi noman masu karfi ne ko wadanda gwamnati ta baiwa tallafi, tun da nake noma fiye da shekarru 20 ban taba shiga cikin wadanda za su amfana da tallafin gwamnati na manoma ba. Tun da gwamnatin tarayya tana son ta mayar da noma madadin fetur a taimakawa manoma musamman a jihohi in za su yi su nemi hakiman fadama” in ji shi. 

Malam Lawali Isa ya ce suna fuskatar karancin abinci a wurarensu karamar Hukumar Isa kan abincinsu da ya bushe ba ruwan sama “Dawarmu ta bushe sosai ba a samu dawa ba a wannan damina shi ne ya sanya mutane suka watse sun tafi ci-rani.”

Aminiya ta zanta da shugaban kungiyar manoma reshen Sakkwato, Alhaji Murtala Gagadu Kan matakin da yake ganin ya kamata gwamnati ta dauka don kaucewa hasashen karacin abinci “Raba kayan noma da wuri matukar gwamnati ta taimakawa manoma da taki da tallafi da wuri za a kaucewa wannan hasashen, gwamna zai kaddamar da rabon taki da wuri amma a rabawa manoma a kananan hukumomi abin ya yi wahala, sai an bata lokaci matukar za a daina sanya wadanda ba su da lokaci a rabon taki masu amana kuma a yanzu da gwamnati ta sayo taki mai dimbin yawa don rabawa manoma, in an same shi da wuri ba wata matsalar karancin abinci da za ta shafi Sakkwato. “Muna godiya ga kokarin da gwamna ke yi kan manoma ya biya kudin jiha don a baiwa manoman alkama da shinkafa bashi, wannan abin yabo ne, saura tallafawa manoman karas da albasa da ayalayyafu da kankana da injin ban ruwa kamar yanda aka yi wa na Alkama da Shinkafa su biya kan dubu 10 da rahusa” a cewar Gagadu.