Manoman shinkafa a Jihar Katsina sun koka kan zabar 

masu cin gajiyar Shirin Anchor Borrower Zargi ya shiga a tsakanin manoman shinkafa na Jihar Katsina kan  hanyar da aka bi ta zaben manoman da za su ci gajiyar shirin ba da rancen kudi na Anchor Borrower Programme a karkashin  Kungiyar Manoman Shinkafa ta Kasa (RIFAN). Da dama daga cikin manoman sun yi korafi kan […]

Manoman shinkafa a Jihar Katsina sun koka kan zabar 

Wata gonar gero

  • masu cin gajiyar Shirin Anchor Borrower

Zargi ya shiga a tsakanin manoman shinkafa na Jihar Katsina kan  hanyar da aka bi ta zaben manoman da za su ci gajiyar shirin ba da rancen kudi na Anchor Borrower Programme a karkashin  Kungiyar Manoman Shinkafa ta Kasa (RIFAN).

Da dama daga cikin manoman sun yi korafi kan yadda aka cire sunayensu daga cikin wadanda za su ci gajiyar shirin duk da yake sun bi duk matakan da suka dace, ciki har da biyan Naira  500 kudin rajista.

Wani daga cikin manoman da ke garin Funtuwa, Umaru Sani, ya ce an karkasa su kungiya-kungiya tun a matakin mazabu kuma kowace kungiya ta kunshi mutum 20 a karkashin babban Kungiyar RIFAN, amma da aka zo wajen daukar bayanai da daukar hoton yatsu wanda aka yi a makonnin baya sai aka ki daukar nasu.

“Mun samu labarin an yi haka ne daga bisani daga wadanda aka riga aka dauki hoton yatsunsu kuma yanzu suna jira ne kawai a ba su kasonsu cikin mako biyu masu zuwa,” inji shi.

Malam Sani  ya ce “Abin takaici ne ganin cewa duk da yake suna da lambobin wayarmu, amma babu wanda ya tuntube mu a kan makomarmu game da wannan shiri. Mafi yawan manoman shinkafa na gaskiya da suke karkara ba su samu shiga ba, ganin yadda aka mayar da tsarin kungiyoyin ya koma kowa yana jawo danginsa da abokansa ne kawai.”

Da yake tofa albarcin bakinsa wani manomi mai suna, Malam Salisu Barebari, cewa ya yi da yawa daga cikin manoman sun ki biyan Naira 500 din da aka ce kowa ya biya saboda tuna abin da ya faru da su a irin wannan shiri da aka yi a baya.

Malam Salisu Barebari ya ce, “A shekara biyu da suka gabata an samu ’yan damfara da dama da suka rika yawo a kauyuka dauke da karamar na’urar kwamfuta  da manyan wayoyi suna karbar Naira 500 zuwa 1000 a matsayin kudin rajista na irin wannan shiri. Amma daga baya muka gano damfara ce kawai, wannan ne ya sanya da yawanmu muke dari-dari da duk wani shiri da Kungiyar RIFAN ta zo da shi, ballantana ma da suka ce sai an biya wata Naira 500.”

Don haka ya shawarci Gwamnatin Tarayya ta gano ingantattun hanyoyin zakulowa tare da taimaka wa sahihan manoma da suke karkara domin suna matukar bukatar tallafin.

Da aka tuntubi Sakataren Tsare-Tsare na Kungiyar RIFAN a Jihar Katsina, wanda kuma shi ne shugaban shiryawa da aiwatar da shirin a jihar, Abubakar Idris Isah cewa ya yi, Naira 500 da manoman suka biya kudin rajista ne da kungiya da kuma kudin takardar shaida na kungiyoyin.

Ya ce “A kashi na farko na wannan shiri da muka aiwatar a baya, an zabi manoma ne a daidaikunsu don haka kungiyarmu ba ta karbi komai ba daga gare su. Amma da yake mun fuskanci matsaloli wajen kin biyan bashin da suka yi, saboda rashin cikakken adireshi, a yanzu sai muka yanke shawarar mu raba su kungiyoyi kowace kungiyar ta kunshi mutum 20. Don haka Naira 500 din, kudin rajistar kasancewa dan kungiya ce da na takardar shaidar kasancewa.”

Da yake bayani kan dalilin da suka sanya wasu manoma ba a dauki hoton yatsunsu ba duk da sun biya Naira 500 din, Isah ya ce kimanin manoma dubu 120 ne a jihar suka nuna sha’awar shiga shirin amma wadanda suka samu nasarar shiga da kadan suka zarce mutum dubu 15,800.

Ya ce, “Mun kai bukatar mutum dubu 120 masu son cin gajiyar shirin ga Bankin CBN, inda daga ciki suka tace wadanda  ba su da lambar shaidar banki ta BBN ko kuma asusun ajiyarsu da lambar BBN dinsu ba su zo daya ba, da kuma wadanda ba su yi rajistar layukan wayarsu ba. Kuma akwai masu taurin bashi a ciki, wadanda ba su biya bashin da aka ba su ba a shirin farko, sannan suka sake nuna sha’awar a kara musu wannan sabo. Daga karshe dai mutum fiye da15,800 wadanda aka dauki bayanan yatsun hannunsu suka yi nasarar shiga wannan shiri daga jihar ta Katsina.”

Ya ce, a wannan karon don samun saukin biyan bashin, kowace kungiya tana da Shugaba da Sakatare da kuma Ma’aji, wadanda aka dora musu alhakin karbo basussukan daga hannun mutum 20 ’ya’yan kowace kungiyar ta manoma.