Manoman shinkafa dubu 50 za su amfana da rancen RIFAN/CBN a Sakkwato
Manoman shinkafa dubu 50 za su amfana daga shirin bayar da rance na RIFAN/CBN Anchor-Borrower da hadin gwiwar Babban Bankin Najeriya (CBN) a Jihar Sakkwato. A wurin kaddamar da rabon kayan amfanin gona da aka yi a jihar karo na uku wakilin Bankin CBN Faruku Abdullahi ya ce, an yi kwakwaran shiri don ganin shirin […]
Manoman shinkafa dubu 50 za su amfana daga shirin bayar da rance na RIFAN/CBN Anchor-Borrower da hadin gwiwar Babban Bankin Najeriya (CBN) a Jihar Sakkwato.
A wurin kaddamar da rabon kayan amfanin gona da aka yi a jihar karo na uku wakilin Bankin CBN Faruku Abdullahi ya ce, an yi kwakwaran shiri don ganin shirin ya samu gagarumar nasara.
Ya ce rabon kayan da za a yi zai fi na baya samun nasara saboda jajircewar da za a yi yadda ba za a samu matsala ba, kamar yadda tabbatar da hakan yayin kaddamarwar.
Shugaban Kungiyar Manoman Shinkafa ta Kasa (RIFAN) reshen Jihar Sakkwato Alhaji Salisu Ibrahim ya yaba wa shirin.
Ya ce da farko an shirya manoman shinkafa dubu 100 za su amfana, amma ya dawo dubu 50 saboda matsalar bin ka’idojin lambar BBN ta banki da wasu manoman suka kasa cikawa.
Shugaban ya ce, rabon kayan zai mamaye kananan hukumomin Sakkwato 23, don haka suka samar da cibiyoyi tara na rabon kayan a kananan hukumomin Goronyo da Sabon Birni da Wurno da Binji da Shagari da Gwadabawa da Tambuwal da Sakkwato ta Kudu da kuma Sakkwato ta Arewa.
Ibrahim ya yaba wa Shugaba Buhari kan kokarinsa na dawo da matabar noma. Ya ce idan Shugaban ya hada kai da manoman shinkafa za a daina shigo da shinkafa zuwa Najeriya.