Manoman shinkafa fiye da dubu 11 sun amfana da rancen noma a jihar Yobe
A kalla ba a kassara ba, manoman shinkafa dubu 11,516 ne suka ci gajiyar shirin tallafa wa manoman rani da Gwamnatin Tarayya ta bayar, a jihar Yobe. Shugaban kungiyar manoman yankin Arewa maso gabas, (NECAS), Onorabul Nuhu Baba, shi ya bayyana hakan, a lokacin kaddamar da rarraba kayakin amfanin gona, karkashin shirin ‘Anchor Borrowers’ da ya […]
A kalla ba a kassara ba, manoman shinkafa dubu 11,516 ne suka ci gajiyar shirin tallafa wa manoman rani da Gwamnatin Tarayya ta bayar, a jihar Yobe.
Shugaban kungiyar manoman yankin Arewa maso gabas, (NECAS), Onorabul Nuhu Baba, shi ya bayyana hakan, a lokacin kaddamar da rarraba kayakin amfanin gona, karkashin shirin ‘Anchor Borrowers’ da ya gudana a Damaturu, babban birnin jihar.
Ya bayyana cewa, shirin rancen manoma na Anchor Borrowers, ya bunkasa noman shinkafa a yankin tare da karfafa gwuiwar manoma da dama, a yankunan kananan hukumomin jihar guda 17.
Kamar dai yadda ya bayyana, manoman shinkafar dubu 11,516, za su noma gonaki masu fadin kadada dubu 19,784. Yace, “A bara, manoma dubu 5002 da suka amfana da shirin, sun noma kadada dubu 11,333.5, a yankunan kananan hukumomi 16. Kuma an karbo kaso 70 cikin dari, na rancen da aka baiwa manoman, ana kuma kokarin amso sauran kasha 30 din da ya rage”.
Ya kara da cewa, wannan shirin da babban bankin Najeriya, CBN, yak e tallafawa tare da bankin masana’antu, ya samar da rarraba kayan aikin noma ga manoman, bias la’akari da bukatunsu, sa’annan za a biya rancen ne, a rubi biyu.
Sai dai yace, da akwai wadansu manoman da aka kama, sakamakon yadda aka same su da yunkurin karkatar da akalar kayayyakin da aka ba sun, kuma a cewarsa, kungiyar ba za ta taba lamuntar hakan ba.
Ya kuma kira ga wadanda suka ci gajiyar shirin da su biya rancen akan kari, don bada damar sake baiwa wasu rancen.
Da yake Magana, babban jami’in raya masu gida-rana, na babban bankin Najeriya a Damaturu, Alhaji Mohammed, ya bayyana takicinsa akan yadda wasu manoman suka rinka sayar da kayayyakin noman da aka ba su, wanda ke da nufin sauya rayuwarsu.
Yace, “Manoma an ba ku wannan rancen ne, wanda dole ne a kanku, ku biya. Idan kun sayar da kayayyakin da aka ba ku, kuma ku ka ki yin noman, to kaka za ku sami damar biyan rancen da ku ka karba”?
Wakilinmu, ya fahimci cewa wasu manoman suna sayar da kayayyakin tallafin noman, akan karamin farashi, kawai dan biyan bukatunsu na yanzu.
Kayayyakin da aka rarraba wa manoman sun hada da, irin da aka inganta na zamani da famfon feshi da taki da injinan ban ruwa da magungunan ciyawa da na kwari.