Manoman sun gamsu kan samun taki a Jihar Nasarawa
A kwanakin baya ne Gwamnatin Jihar Nasarawa ta raba wa manoman rani a jihar takin zamani. Gwamnatin ta sayar wa manoman takin ne a kan Naira dubu hurhudu kowane buhu. Jim kadan da raba takin wakilinmu ya zanta da wadansu daga cikin manoman a jihar inda suka bayyana ra’ayoyinsu dangane da raba takin da kuma farashin […]
A kwanakin baya ne Gwamnatin Jihar Nasarawa ta raba wa manoman rani a jihar takin zamani. Gwamnatin ta sayar wa manoman takin ne a kan Naira dubu hurhudu kowane buhu. Jim kadan da raba takin wakilinmu ya zanta da wadansu daga cikin manoman a jihar inda suka bayyana ra’ayoyinsu dangane da raba takin da kuma farashin kamar haka.
Aliyu Shu’aibu Adamu manomin rani ne da ke zaune a Lafiya babban birnin jihar, inda a zantawarsa da wakilinmu ya ce: “A gaskiya ina farin ciki matuka dangane da karamcin da gwamnanmu mai son ci gaban manoma da kuma harkar noma a jihar dangane da hangen nesan da ya yi na raba mana takin wanda kamar yadda ka sani wannan shi ne karo na farko da gwamnati a jihar nan ta yi mana haka. Kuma ba shakka hakan zai ba mu damar bunkasa harkokin nomanmu na rani a bana. Kuma a karshe za a samu issashen abinci a jihar nan.’’
Sai ya yi kira ga gwamnatin ta sauke farashin takin: “Ina nufi a rika sayar da kowane buhu Naira 3,500 ko kasa da haka, don mu samu damar saye da yawa. A yanzu ba kudi a hannun manoman rani,” inji shi.
Ya yi kira ga gwamnatin ta duba batun samar da babban filin noman rani a jihar musamman na noman shinkafa da masara kamar yadda ya ce gwamnatin ta yi alkawari kwanakin baya. “Da a ce ina da babban fili da na rika noma shinkafa da masarar da ake shukawa da rani da aka raba mana da sauransu. Don a gaskiya ba ni kadai ba akwai mutane da dama da suke sha’awar noman rani a jihar nan; amma saboda rashin filin noman ya sa ba sa cimma wannan buri,” inji shi.
Shugaban Al’ummar Hausawa yankin Jenkwe a Karamar Hukumar Obi a jihar kuma Sarkin Noman yankin, Alhaji Adamu Usman ya shaida wa Aminiya cewa: “A gaskiya, ina wajen rabon takin zamanin na noman rani da gwamnati ta raba; kuma a bincike da na gudanar bayan rabon na gano cewa galibin manoman rani a jihar nan sun amfana da takin.”
“Akwai alfanu sosai a noman rani, saboda haka dole a bada fifiko ga fannin don idan aka dogara ga noman damina kawai ba za a iya samar da abinci yadda ake bukata ba. A takaice sai hamdala bana, domin ba mu da matsalar takin noman rani a jihar nan, ba kamar yadda lamarin ya kasance a baya ba. Kuma ina kiran manomanmu na rani su tabbatar sun yi amfani da takin; ba su rika sayar da shi ba. Domin in gwamnati ta samu labarin suna sayar da takin ba za ta ji dadin haka ba. Kuma nan gaba ba za ta sake tallafa musu ba,” inji shi.