‘Manomi da Tsuntsaye’
Barkanmu da warhaka Manyan gobe tare da fatan ana lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Manomi da tsuntsaye’. Labarin ya yi nuni ne da yadda babu tabbacin faruwar wani abu har sai mutum ya yunkura kuma ya yi wa kansa. A sha karatu lafiya. Taku, Amina Abdullahi. Akwai wani manomi wanda yake da gonar […]
Barkanmu da warhaka Manyan gobe tare da fatan ana lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Manomi da tsuntsaye’. Labarin ya yi nuni ne da yadda babu tabbacin faruwar wani abu har sai mutum ya yunkura kuma ya yi wa kansa. A sha karatu lafiya.
Taku, Amina Abdullahi.
Akwai wani manomi wanda yake da gonar masara. Gonar tasa tana da girma don haka ya dauki tsawon watanni wajen shuka masarar.
A cikin gonar akwai wani tsuntsu tare da ’ya’yansa sun yi gidansu suna shakatawa. Sun dauki alkawarin barin wannan bishiyar zuwa wata a duk lokacin da manomin zai yi girbi saboda kada garin yin girbi ya hada da su.
Ran nan sai suka ji manomi yana cewa gobe zai girbe gonarsa. Hankalin ’ya’yan tsuntsu suka tashi da cewa su bar wajen amma mahaifinsu ya kwantar musu da hankali cewa ba zai iya girbe gonar duka a gobe ba. Hakan kuma aka yi.
Sai suka saka ji yana fadin cewa gobe ’yan’uwansa za su taya shi girbe masara duk da haka hankalin tsuntsayen bai tashi ba ya sake kwantar wa ’ya’yansa hankali cewa babu abin da zai faru.
Washegari manomi yana ta jira amma bai ga kowa daga wadanda za su taimaka masa wajen yin girbi ba sai ya fada wa ’ya’yansa cewa kun ga abin da na fada muku ya zama gaskiya ko?
Bayan manomi ya gama zama a gonarsa har yamma bai ga kowa ba ne sai suka ji yana cewa gobe dai zai girbe gonarsa duka da kansa. Jin hakan ya sa tsuntsayen suka yanke shawarar yin hijira zuwa wata gona.
Tare da fatan Manyan Gobe za su dauki darasi daga wannan labari. Babu wanda zai yi maka aikinka fiye da kai don haka ina fata za ku kasance masu kwazo da hazaka wajen yin ayyukansu da kanku.