‘Manomi da tsuntsaye’
Barkanmu da warhaka Manyan Gobe. Yaya sanyi? Da fatan ana sanya rigunan sanyi idan za a tafi makaranta. A yau zan kawo muku wani labari ne mai taken: ‘Manomi da tsuntsaye’. Labari ne da ya kunshi muhimmancin yin aboki nagari don a samu shaida mai kyau. Akwai wani manomi ne wanda kullum tsuntsaye sai sun […]
Barkanmu da warhaka Manyan Gobe. Yaya sanyi? Da fatan ana sanya rigunan sanyi idan za a tafi makaranta. A yau zan kawo muku wani labari ne mai taken: ‘Manomi da tsuntsaye’. Labari ne da ya kunshi muhimmancin yin aboki nagari don a samu shaida mai kyau.
Akwai wani manomi ne wanda kullum tsuntsaye sai sun yi masa barna a gona, abin ya dame shi sai ya dana tarko a gonarsa. Washegari, sai ya je gonarsa don ya ga irin tsuntsayen da ke masa barna a gona. Da manomi ya je gona, sai ya ga tsuntsaye da yawa a cikin tarko. Sai ya ce zai kashe su. Nan take sai daya daga cikin tsuntsayen ya fara kuka yana cewa “Don Allah ka sake ni, wallahi ban yi maka barna a gona ba, ni dan kirki ne kuma ina girmama iyayena…”.
Sai manomi ya katse shi ya ce “Yi mana shiru! Zai yiwu kana da gaskiya amma yaya aka yi na same ka a tarko tare da masu yi mini barna a gona? An ce ‘abokin barawo, barawo ne’. Saboda haka sai na hallaka ka da wadanda na kama ku tare.” Daga nan manomi ya kashe wannan tsuntsun tare da sauran ba tare da ya yi masa uzuri ba.
Da fatan Manyan Gobe za su dauki darasi a cikin wannan labarin. Kuma za su san irin abokan da za su rika mu’amula da su domin an ce ‘abokin barawo, barawo ne’.
Taku; Gwaggo Amina Abdullahi