Manomi ya fi malami – Ustaz Tilde5

Malami na da matukar muhimmanci ga al’umma, musamman saboda haskaka su da yake yi da ilimi. Haka shi ma manomi, yana da nasa amfanin, musamman yadda yake wahala domin samar da abinci; kasancewar Hausawa sun ce sai da ruwan ciki sannan ake jan na rijiya. Abin tambaya a nan shi ne, shin tsakanin wadannan mutane […]

Manomi ya fi malami – Ustaz Tilde5
Manomi ya fi malami – Ustaz Tilde5

Malami na da matukar muhimmanci ga al’umma, musamman saboda haskaka su da yake yi da ilimi. Haka shi ma manomi, yana da nasa amfanin, musamman yadda yake wahala domin samar da abinci; kasancewar Hausawa sun ce sai da ruwan ciki sannan ake jan na rijiya. Abin tambaya a nan shi ne, shin tsakanin wadannan mutane biyu, wane ne ya fi amfani ga al’umma? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:

Ustaz Muhammad A.A. Tilde: “Idan aka dauki amfaninsu za a rinjayar da malami ne a kan manomi amma kowane malami manomi ne sai dai ba kowane manomi ba ne malami. Amma idan aka koma kan amfaninsu, za ka ga cewa shi malami ya takaita ne kawai a kan karantarwa. Shi malami yana gina kwakwalwa ne ko ruhi amma shi kuma manomi yana gina jiki ne. Shi kuwa ilimi ba ya zama idan jiki bai ginu ba. Shi ya sa lokacin da Allah Ya sauko Annabi Adam sai Ya fara da karantar da shi ilimin sana’a domin ya ci abinci. Amma a can sama kuma an karantar da shi ne ilimin fifiko wanda da shi ya sa ya yi wa mala’iku zarra. Shi ya sa idan muka dube su baki daya sai mu ga cewa duk suna da amfani amma dai manomi ya fi amfanar al’umma ta wani barin. Domin malami kan dogara ne ga abin da manomi ya shuka. Shi kuma ta wajen tasiri malami ya fi. Shi ya sa ake ganinsu kamar iska ne da ruwa, ba za ka iya cewa ga wanda ya fi amfani ba.”

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50